Zaben 2019: Matasa ne suka fi bayar da kunya - Dan takarar shugaban kasa

Zaben 2019: Matasa ne suka fi bayar da kunya - Dan takarar shugaban kasa

Dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar Young Progressive Party (YPP), Farfesa Kingsley Moghalu ya cacaki matasan Najeriya a kan irin rawar da suka taka yayin babban zaben shekarar 2019.

A hirar da akayi da shi a Channels TV a wani shiri mai suna Politics Today, Moghalu ya ce ya ji takaicin yadda matasa ba su fito sun taka muhimmiyar rawar da ya dace ba a yayin zaben.

"Matasa sun bani kunya sosai. Sun dade suna hayaniya suna ta cika baki amma a ranar zabe sai aka neme su aka rasa. Kuma a inda su kayi zabe, ba suyi zabe bisa akidar da suka rika magana a kai ba," inji shi.

Zaben 2019: Matasa ne suka fi bayar da kunya - Dan takarar shugaban kasa
Zaben 2019: Matasa ne suka fi bayar da kunya - Dan takarar shugaban kasa
Source: Instagram

DUBA WANNAN: Saurayi ya kashe wacce zai aura saboda ta raina girman mazakutarsa

Da ya ke tsokaci a kan nasarar da shugaba Muhammadu Buhari ya samu a zaben na 2019, Moghalu ya shawarci shugaban kasar ya sakawa al'ummar Najeriya bisa kuri'un da suka bashi.

Ya ce yana son gwamnatin tarayya ta mayar da hankali a kan bangarori uku; hadin kan 'yan kasa, inganta tattalin arziki da kuma magance kallubalen tsaro da ake fama da shi a sassa da dama na kasar.

Da ya ke tsokaci a kan tsaro, ya yi koka kan yadda gwamnati ba ta ware isasun kudade ga rundunar 'yan sandan Najeriya domin su samu makamai na zamani da zai tallafa musu wurin kiyaye lafiya da dukiyoyin al'umma.

Tsohon mataimakin shugaban bankin kasa, CBN ya kuma ce yana goyon bayan cire tallafin man fetur a Najeriya. Ya kuma ce yana son a sayar da hukumar NNPC ga 'yan kasuwa domin a halin yanzu ba a tafiyar da harkokin cikin tsari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel