Ikirarin jam’iyyar APC akan tushena sakarci ne – Atiku

Ikirarin jam’iyyar APC akan tushena sakarci ne – Atiku

Dan takarar Shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben 2019, kuma tsohon mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar ya yi watsi da rubutaciyyar karar da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta shigar da ke hamayya da asalinsa a matsayin sakarci.

Atiku wanda yayi magana ta hannun hadimin labaransa, Paul Ibe, ya fada ma jaridar Sun, a jiya Juma’a, 12 ga watan Afrilu, cewa wannan cin mutunci ne ga yan Najeriya da ofishin mataimakin Shugaban kasa, wanda ya shafe shekaru takwas akai, sannan a yanzu APC ta dauko wannan zargi a kansa cewa ba dan Najeriya bane.

Ikirarin jam’iyyar APC akan tushena sakarci ne – Atiku

Ikirarin jam’iyyar APC akan tushena sakarci ne – Atiku
Source: Facebook

Yace ba komai ya kamata a siyasantar ba. A cewarsa, “Sakarci ne. Kuma abun dariya ne. Atiku Abubakar ya kasance tsohon mataimakin Shugaban kasar Najeriya. Shin suna fada mana cewar tsohon mataimakin Shugaban kasar jumhuriyar Najeriya ba dan Najeriya bane? Wannan rashin girmamawa ne ga yan Najeriya da kuma mukamin da ya rike, wanda sauran mutane za su rika sannan a ci gaba da rika. Ba komai ya kamata a sa siyasa a ciki ba.”

Duk kokarin da aka yi domin jin maratanin Shugaban PDP akan lamarin, ya ci tura a daidai lokacin wannan rahoton, domin babban sakataren labaran jam’iyyar na kasa, Kola Ologbodiyan bai amsa kiran wayarsa ba.

KU KARANTA KUMA: Hanashi takarar gwamna: Kotu ta yi watsi da karar da Ministan sadarwa, Shittu ya shigar kan APC

A baya Legit.ng ta rahoto cewa, Jam'iyyar All Progressive Congress (APC) ta shigar da kara kotun zaben shugaban kasa dake Abuja cewa dan takaran shugaban kasan jam'iyyar People’s Democratic Party PDP, Atiku Abubakar, ba dan Najeriya bane saboda haka bai cancanta yayi takarar zaben ba.

Jam'iyyar ta yi ikirarin cewa tsohon mataimakin shugaban kasan dan kasan Kamaru ne kuma ba dan Najeriya bane, saboda haka, kotu tayi watsi da karar da ya shigar na kalubalantan nasarar da shugaba Muhammadu Buhari, a zaben 2019.

Bugu da kari, jam'iyyar APC ta bukaci kotun zabe ta watsar da kuri'u miliyan goma sha daya da Atiku ya samu a zabe saboda bai kamata dan wani kasa daban yayi takara a zaben Najeriya ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel