Sai na kawo karshen ta’addanci a Najeriya – Shugaban yan sanda ya dau alkawari

Sai na kawo karshen ta’addanci a Najeriya – Shugaban yan sanda ya dau alkawari

Sufeto janar na yan sanda, Mohammed Adamu, ya bayyana cewa sai ya kawo karshen aikata laifuka a jihohi daban-daban na fadin Najeriya.

Adamu yayinda yake yaba ma jami’an rundunar yan sandan Najeriya akan nasarar da suka samu wajen yaki da laifuyka a kasar yace yan sanda na aiki tare da sauran hukumomin tsaro.

Ya kuma ce yan sanda ba za su huta ba har sai sun kore duk matsalar sace-sacen mutane da sauran laifuka, sannan su dawo da zaman lafiya a kasar.

Vanguard ta ruwaito cewa Shugaban yan sandan yayi wannan alkawarin ne bayan kama bokan masu garkuwa da mutane day an fashi da ke ta’addanci a yankin arewacin kasar.

Sai na kawo karshen ta’addanci a Najeriya – Shugaban yan sanda ya dau alkawari
Sai na kawo karshen ta’addanci a Najeriya – Shugaban yan sanda ya dau alkawari
Source: Twitter

Yan sandan sunce an kama Mallam Salisu Abubakar da taimakon jami’an Operation Puff Adder bayan bayanai daban-daban, da kuma bincike.

Har ila yau an kama masu satar mutane 18 da yan fashi a lokuta da wurare daban-daban a fadin kasar.

KU KARANTA KUMA: Masu damfarar mutane a Kasar Amurka daga Najeriya sun fada hannun hukuma

An kuma tattaro cewa an samu bindigar AK 47 22, bindigun gargajiya da kuma alburusai daga mafakar yan bindigan a dajin Birnin Gwari, Rijana, Katari, Mai Daro da kuma Buruku a jihar Kaduna.

Masu laifin na da annu a wasu manyan laifuka da aka aikata a jihar Kaduna da kewayenta yan kwanakin baya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel