Hukumomin tsaro sun binciko wata makarkashiya da Atiku ya ke hadawa Buhari

Hukumomin tsaro sun binciko wata makarkashiya da Atiku ya ke hadawa Buhari

Rahotanni sun nuna cewa hukumomin tsaron Najeriya sun binciko wata makarkashiya da dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar ya ke hadawa shugaban kasa Muhammadu Buhari, domin kawar dashi daga mulki

Hukumomin tsaron Najeriya sun gaano wata makarkashiya da dan takarar shugaban kasa jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya ke yi wa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Hukumomin yanzu haka suna bincikar wasu kungiyoyi na masoya Atiku Abubakar din, akan hotunan Atiku da aka saka a wasu sassa na kasar nan.

Mun samu labarin cewa hukumomin tsaro sun binciko wasu kungiyoyi masu biyayya ga Atiku, suna fito na fito da mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Hukumomin tsaro sun binciko wata makarkashiya da Atiku ya ke hadawa Buhari

Hukumomin tsaro sun binciko wata makarkashiya da Atiku ya ke hadawa Buhari
Source: Depositphotos

Bayan makarkashiyar da Atikun ya ke hadawa wurin neman goyon bayan wasu daga cikin 'yan majalisar shugaban kasar Amurka Donald Trump, akan kada su bayyana shugaba Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa a Najeriya. An bayyana cewa Atiku ya na so ya yi amfani da wannan damar ce wurin kawo cikas a wurin rantsar da shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar 29 ga watan Mayu.

KU KARANTA: Atiku na cikin tsaka mai wuya

Bayan Atiku da jam'iyyar PDP sun karyata zargin da ake yi musu, sai ga wani rahoto kuma an samu da ke nuna shaidar lokacin da Atiku ya biya sojojin haya dala 30,000, domin ta ya shi yakin kwace zabe daga wurin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Wata majiya mai karfi ta bayyana cewa an samu kwararan shaidu da ke nu na irin makarkashiyar da ake hadawa shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda a yanzu haka hukumomin tsaro suna gabatar da bincike akan lamarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel