Zaben Rivers: Yan sanda sun hana zirga-zirga a kananan hukumomi 4

Zaben Rivers: Yan sanda sun hana zirga-zirga a kananan hukumomi 4

Rundunar yan sandan jihar Rivers ta tsaurara matakan tsaro sannan ta hana zirga-zirga a kananan hukumomi hudu da ke jihar inda za a sake gudanar da zabe a yau Asabar, 13 ga watan Afrilu.

DSP Nnamdi Omoni, kakakin rundunar yan sandan ya bayyana hakan a wani jawabi da ya saki a Port Harcourt.

Omoni ya bayyana cewa an tanadi isashen tsaro domin tabbatar da gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da lumana, da kuma hana barkewar rikici.

An tattaro cewa kananan hukumomin da za a gudanar da shirin sun hada da Abua/Odual, Ahoada-West, Gokana da kuma Opobo/Nkoro da ke jihar.

Zaben Rivers: Yan sanda sun hana zirga-zirga a kananan hukumomi 4

Zaben Rivers: Yan sanda sun hana zirga-zirga a kananan hukumomi 4
Source: Depositphotos

Ya bayyana cewa Mista Usman Belel, kwamishin yan sandan jiar Rivers da Shugaban kwamitin tsaron zabe ne suka bayar da umurnin bayan tattaunawa da suka yi.

Yace kwamishinan ya kuma yi umurnin cewa a toshe dukkanin mashigi da mafitar wadannan kananan hukumomi da abun ya shafa har zai an kamala zabe sannan kada a bari a tafiyar da ayyukan ciniki a kusa da mazabu.

KU KARANTA KUMA: Tirkashi: An kama tsohon shugaban karamar hukuma da laifin zina da matar makwabcin sa

Kakakin rundunar yace hukumar da sauran hukumomin tsaro za su yi ta sintiri don tabbatar da bin doka da oda sannan a kama duk wanda ya karya doka a kuma hukunta masu tayar da zaune tsaye.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel