Zargin zamba: Kotu ta ki ci gaba da shari’an Babachir Lawal

Zargin zamba: Kotu ta ki ci gaba da shari’an Babachir Lawal

Shari’an Babachir Lawal, tsohon babban sakataren tarayya, da wasu mutane uku kan zargin zambar naira miliyan 544 ya samu cikas saboda alkalin da ke shari’an bai hallara a kotu ba.

Lawal na fuskantar tuhuma akan rashawa. An tuhume shi da amfani da kamfaninsa wajen samun kwangila na miliyoyin naira ba tare da ya aiwatar da kwangilan ba.

An gurfanar dashi tare da Hamidu David, Suleiman Abubakar da wasu kamfanoni biyu Rholavision engineering Ltd da Josmon Technologies Ltd kan tuhume-tuhume 10 da ya hada da damfara.

Zargin zamba: Kotu ta ki ci gaba da shari’an Babachir Lawal

Zargin zamba: Kotu ta ki ci gaba da shari’an Babachir Lawal
Source: UGC

An sauke shi daga mukaminsa na sakataren tarayya bayan kwamitin majalisar dattawa da tayi binciken yadda aka gudanar da kudin da ya kamata a tallafa wa yan gudun hijira da harin Boko Haram ya ritsa da su ta same shi da hannu dumu-dumu a lamarin.

Sai dai kuma, Babachir da wadanda ake zarginsu tare sun ki amsa laifinsu sannan aka bayar da belinsu kan kudi naira miliyan 50.

A ranar 18 ga watan Maris, biyo bayan gyare-gyaren tuhumar daga hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), kotu ta dage shari’an zuwa ranar 11 ga watan Afrilu.

KU KARANTA KUMA: Ka duba kwararru a yayin kafa sabuwar majalisa – Ganduje ga Buhari

Sai dai kotu bata zauna ba a ranar saboda rashin hallaran Justis Jude Okeke, alkain shari’an.

Biyo bayan yarjejeniya daga lauyan mai kara da wanda ake kara, kotu ta sanya ranar 23 ga watan Mayu a matsayin sabon ranar sauraron shari’an.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel