Zabe: Rundunar yan sanda ta tura jami’ai 3,066 zuwa jihar Rivers

Zabe: Rundunar yan sanda ta tura jami’ai 3,066 zuwa jihar Rivers

Rundunar yan sandar jihar Rivers ta tura jami’ai 3,066 wasu yankunan da za a sake zabe a jihar a ranar Asabar, 13 ga watan Afrilu.

Kakakin rundunar yan sandan, DSP Nmandi Omoni, ya bayyana hakan a wata sanarwa a Port Harcourt a ranar Juma’a, 12 ga watan Afrilu.

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) a ranar 21 ga watan Maris, ta sanar da shirye-shiryen sake gudanar da zabe a kananan hukumomin Abua/Odua, Ahoada West, Gokana da Opobo/Nkoro da ke jihar.

A cewar Omoni, hukumar yan sanda da sauran hukumomin tsaro sun shirya domin samar da ingantaccen tsaro don tabbatar da zabbe cikin lumana.

Zabe: Rundunar yan sanda ta tura jami’ai 3,066 zuwa jihar Rivers

Zabe: Rundunar yan sanda ta tura jami’ai 3,066 zuwa jihar Rivers
Source: UGC

Omoni ya bayyana cewa za a hana zirga-zirga a kananan hukumomin da abun ya shafa daga karfe 11:59 na safiyar ranar Juma’a zuwa karfe 2:00 na ranar Asabar.

KU KARANTA KUMA: Lawal, Ndume, Goje, duk sun cancanci jagorantar majalisar dattawa – Jigon APC

Kakakin yan sandan yayi gargadin cewa za a kama duk wani mutun ko kungiya da aka gani yana kaskatar da tsarin zabe sannan a hukunta shi daidai da dokar zabe.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Jam'iyyar All Progressives Congress, APC reshen Jihar Rivers tayi Allah wadai da dokar hana zanga-zanga da tattaki da gwamnan jihar Rivers, Nyesome Wike ya saka a jihar.

Jam'iyyar ta fitar da sanarwar ne cikin wata sako da sakataren yada labarai na jam'iyyar, Mr Chris Finebone ya fitar a garin Fatakwal. A martanin da tayi, jam'iyyar APC ta ce wannan dokar da gwamnan jihar ya saka "tsabar hauka ne".

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel