An kama wasu daliban jami’a 2 suna zanama wani jarabawar JAMB

An kama wasu daliban jami’a 2 suna zanama wani jarabawar JAMB

Ma'aikatar JAMB ta bayyana cewa ta kama wani dalibin aji uku a fannin ilimin kiwon lafiya da kuma wani dan jami’a suna yunkurin rubuta ma wadanda za suyi jarabawar JAMB na bana.

Babban shugaban sashin labarai na kungiyar, Dr Fabian Benjamin ya bayyana hakane a wani tattaunawa da yayi da NAN a ranar jumaa a jihar Lagos.

NAN ta bada rahoto cewa an fara jarabawar JAMB dinne a ranar 11 ga watan Aprilu a cibiyoyi 678 a kasar .

KU KARANTA: Karar Zaben 2019: Atiku ba dan Najeriya bane - APC ta bayyanawa kotu

Benjamin ya bayyana cewa, duk da cewar an jajirce wurin ganin cewar an kauda duk abinda zai kawo sata a jarabawar amma duk a banza sai da wasu suka yi yunkurin yin hakan.

Yace: "An kama wata budurwa a daya daga cikin cibiyar jarabawar a Jihar Kano tana kokarin zama domin ta zana ma daya daga cikin masu jarabawar."

Yayinda aka gudanar da bincike, an gano cewa budurwar dalibace a bangaren kiwon lafiya a jami’ar Usman Dan fodio dake Sokoto."

Ya bayyana ma NAN cewa an kara kama wani a Jihar Benin,wanda dalibi ne a jami’ar jihar.

A karshe yace: "Ma'aikatarmu ba zata lamunci irin wadannan alamuran da zasu kawo tangarda ba da nagarta wurin gudanar da jarabawar."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel