Ka duba kwararru a yayin kafa sabuwar majalisa – Ganduje ga Buhari

Ka duba kwararru a yayin kafa sabuwar majalisa – Ganduje ga Buhari

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya shawarci Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya nemi masu nagarta a yayin kafa sabuwar majalisarsa.

Ganduje ya bayar da wannan shawarar ne yayin amsa tambayoyi daga manema labarai na fadar Shugaban kasa, bayan wata ganawar sirri da mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo a ranar Juma’a, 12 ga watan Afrilu a fadar Shugaban kasa da ke Abuja.

Yace ya je fadar Shugaban kasa ne domin sanar da mataimakin Shugaban kasa cewa an kamala komai domin ziyarar da zai kai jihar Kano a ranar Asabar, 13 ga watan Afrilu domin halartan wani bikin aure.

Ka duba kwararru a yayin kafa sabuwar majalisa – Ganduje ga Buhari

Ka duba kwararru a yayin kafa sabuwar majalisa – Ganduje ga Buhari
Source: UGC

Ganduje yace ya kuma sanar da Osinbajo cewa mutanen Kano sun shirya tarbansa yayinda suke farin ciki da cewar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta lashe zabe a jihar.

Ya kuma bayyana cewa baya dar-dar don jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta shiga kotun zabe don kalubalantar sakamakon zaben gwamna a jihar.

KU KARANTA KUMA: Bauchi: APC ta gabatar da rubutacciyar kara don kalubalantar nasarar Sanata Bala

Ganduje ya bayyana cewa wasu jam’iyyun siyasa a jihar sun hade don shiga yarjejeniyar fahimta da jam’iyyarsa, inda ya kara da cewa za a wanzar da aminci har zuwa ga PDP.

Gwamnan ya bayyana cewa ya gina tubali mai karko don ci gaban jihar, musamman a fannin ababen more rayuwa, ilimi da kuma lafiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel