Boko Haram sun mayar da yara sama da 3,500 yan ta’adda a arewa maso gabas – UNICEF

Boko Haram sun mayar da yara sama da 3,500 yan ta’adda a arewa maso gabas – UNICEF

Kungiyar UNICEF ta bayyana cewa kimanin yara sama 3,500 ne ‘yan ta’adda suka tilastawa yin yakin sari-ka-noke a yankin arewa maso gabashin kasar Najeriya.

UNICEF ta ci gaba da cewa bisa tilas aka ta horas da su tare da koya musu atisayen kai hare-hare tun daga shekarar 2013.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce yaran wadanda mafi akasarinsu suka kasance daga shekaru 13 zuwa 17, an horas da su ne tsakanin 2013 zuwa 2017, kuma da su ake ta gumurzun yake-yake da hare-haren da ake yi a yankin arewa maso gabashin kasar.

Haka dai UNICEF ta bayyana a yau Juma’a, 12 ga watan Afrilu da safe, ta hannun daya daga cikin manyan jami’an ta, mai suna Eva Hinds.

Boko Haram sun mayar da yara sama da 3,500 yan ta’adda a arewa maso gabas – UNICEF

Boko Haram sun mayar da yara sama da 3,500 yan ta’adda a arewa maso gabas – UNICEF
Source: UGC

Yayin da suke jimamin ranar cikar kama daliban Chibok shekaru biyar, Majalisar Dinkin Duniya ta hannun UNICEF, ta ce wadannan adadin yara 3,500, ba kirdado ko kintace ba ne, bincike ya tabbatar da an horas da su din. UNICEF ta ce zai iya yiwuwa ma adadin ya zarce haka.

KU KARANTA KUMA: Bauchi: APC ta gabatar da rubutacciyar kara don kalubalantar nasarar Sanata Bala

Baya ga wadanda aka horas, UNICEF ta kara da cewa a cikin 2018 kadai an karkashe kananan yara har 432, an sace 180, sannan kuma an yi wa kananan yara mata 43 fyade, duk a Arewa maso Gabas.

Sannan kuma UNICEF ta ce har yau ba a daina tilasta wa mata auren wadanda suka sace su ba, tun daga 2012 har zuwa yau.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel