Karar Zaben 2019: Atiku ba dan Najeriya bane - APC ta bayyanawa kotu

Karar Zaben 2019: Atiku ba dan Najeriya bane - APC ta bayyanawa kotu

Jam'iyyar All Progressive Congress (APC) ta shigar da kara kotun zaben shugaban kasa dake Abuja cewa dan takaran shugaban kasan jam'iyyar People’s Democratic Party PDP, Atiku Abubakar, ba dan Najeriya bane saboda haka bai cancanta yayi takarar zaben ba.

Jam'iyyar ta yi ikirarin cewa tsohon mataimakin shugaban kasan dan kasan Kamaru ne kuma ba dan Najeriya bane, saboda haka, kotu tayi watsi da karar da ya shigar na kalubalantan nasarar da shugaba Muhammadu Buhari, a zaben 2019.

Bugu da kari, jam'iyyar APC ta bukaci kotun zabe ta watsar da kuri'u miliyan goma sha daya da Atiku ya samu a zabe saboda bai kamata dan wani kasa daban yayi takara a zaben Najeriya ba.

Lauyoyin APC karkashin jagorancin, Lateef Fagbemi, sun kalubalanci takarar Atiku a zaben saboda dan kasar Kamaru ne, bai ma kamata ace ya yi takara a zaben ba.

KU KARANTA: Da duminsa: Buhari zai ziyarci kasar Chadi ranar Asabar

Ya ce an haifi Atiku ranar 25 ga watan Nuwamba, 1946 a Jada, Adamawa wacce take Arewacin kasar Kamaru, saboda haka, ba haifaffen dan kasar Najeriya bane.

Bisa ga tarihi, APC ta bayyana cewa gabanin shekarar 1919, Kamaru na karkashin mulkin mallakan Jamus kafin kayin da ta samu yakin duniya ta farko. Bayan yakin da ta kare a 1918, Kamaru ta koma karkashin mulkin mallakan kasar Faransa da Birtaniya.

APC ta bayyana cewa a shekarar 1961, an yi zabe kan shin Kamaru dake karkashin mulkin mallakan Birtaniya na son haduwa da Najeriya ko za ta hadu da Kamaru dake karkashin mulkin Faransa.

A lokacin, Kamaru ta Arewa ta zabi kasancewa da Najeriya, hakan ya shigo da Adamawa Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel