Najeriya za ta ci gaba da tallafa wa makwabtanta - Buhari

Najeriya za ta ci gaba da tallafa wa makwabtanta - Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Juma’a, 12 ga watan Afrilu ya bayyana cewa a koda yaushe Najeriya za ta ba makwabtanta hadin kai da taimako a inda bukatar hakan ya taso.

Shugaban kasar wanda ya bayyana hakan yayinda ya karbi bakuncin jakadan Equatorial Guinea, Mista Job Obiang Esono Mbengono, a taron ban kwana a fadar shugab kasa, Abuja, yace Najeriya da Equatorial Guinea na da alaka mai kyau a tsakaninsu, “kuma za su ci gaba da makwabtaka mai nagarta.”

Shugaba Buhari yace yayi farinciki da cewar jakada mai baring ado, wanda ya kwashe shekaru tara a Najeriya, “ya zauna kuma ya fahimci al’adun mutanenmu sosai."

Najeriya za ta ci gaba da tallafa wa makwabta - Buhari

Najeriya za ta ci gaba da tallafa wa makwabta - Buhari
Source: UGC

Ambasada Mbengono, yace Najeriya ta taka gagarumin rawa a rayuwarsa, kamar yadda ya koyi abubuwa da dama “game da wannan babban kasa mai muhimmanci,” ya kara da cewa mutanen kasar na da fara’a da son mutane.

KU KARANTA KUMA: Bai dace ba ga kowane asibiti su ki karbar wanda suka samu hadari, inji hukumar kiyaye hadurra ta FRSC

Da yake taya shugaba Buhari murnar sake lashe zabe, yace “Najeriya na a hannu nagari, kuma muna farin ciki."

Jakadan ya kuma isar da fatan alkhairin Shugaban kasa Teodoro Obiang Nguema Mbasogo ga shugqaban Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel