Hanashi takarar gwamna: Kotu ta yi watsi da karar da Ministan sadarwa, Shittu ya shigar kan APC

Hanashi takarar gwamna: Kotu ta yi watsi da karar da Ministan sadarwa, Shittu ya shigar kan APC

-Kotu ta yi watsi da karar da Ministan sadarwa ya shigar kan jam'iyar APC

-Hakan ya biyo bayan saba doka da akayi wajen shigar da karar a gaban kotu

Wata babbar kotun tarayya ta kasa a garin Ibadan ce ta kori wannan karar da ministan na sadarwa keyi akan jami’iyar APC bisa ga cire sunanshi da jam’iyar tayi daga jerin sunayen masu takarar gwamnan zaben 2019 a karkashin jam’iyar APC saboda bai kawo takardar shaidar kammala bautar kasa ba (NYSC).

Jam’iyar ta hana Shittu kasancewa daya daga cikin yan takarar da za suyi zaben fidda gwani saboda bai yi bautar kasa ba bayan kammala karatunsa na jami’a.

Adebayo Shittu

Adebayo Shittu
Source: Twitter

KARANTA WANNAN:Gwamnatin tarayya zata tilastawa masu gidajen man fetur siyar da gas din girki

Da take nata hukuncin, Mai shari’a P.I Ajoku tace sunyi watsi da wannan karar ne saboda rashin kawota gaban kotu akan kari da Shittu bai yi ba bisa ga lokacin da doka ta kayyade.

“Ya zama wajibi a gareni in yi la’akari da kundin tsari a karkashin sashe na dari biyu da tamanin da biyar (285) ya wajabta lallai duk wasu matsaloli da suka kunshi rikita-rikitar gabanin zabe to tilas ne a shigar da karar tasu cikin kwanaki goma sha hudu kafin zaben.

“Wannan karar kuwa ba a shigar da ita ba cikin kwanaki goma sha hudun da doka ta tanadar ba sai dai bayan wucewar wannan wa’adi. Saboda haka ban damu kaina da sai na bi diddigi akan wannan kara ba.”

“Bisa ga sabawa doka da akayi wajen kawo wannan kara, hakan shine yayi sanadiyar kotunmu ta kori wannan kara da gabanta,” Mai shari’ar ta yanke hukunci.

Da yake martani akan wannan abu, Lauyan dake kariyar wanda ake tuhuma mai suna, Adebayo Ojo wanda shine tsohon Kwamishinan shari’a na jihar Oyo, yace shari’a ta riga da tayi aikinta.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel