Da duminsa: Buhari zai ziyarci kasar Chadi ranar Asabar

Da duminsa: Buhari zai ziyarci kasar Chadi ranar Asabar

Shugaba Muhammadu Buhari zai tafi garin N'Djamena babban birnin kasar Chadi a ranar Asabar 13 ga watan Afrilun 2019 a cewar wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar.

Shugaban kasan zai tafi Chadi ne domin hallartar wata muhimmiyar taron shugabanin kasashen da ke yankin Sahel Sahara, CEN-SAD.

Sanarwar da Kakakin shugaban kasa, Garba Shehu ya fitar da ce shugaba Buhari zai dawo Najeriya a ranar Asabar din bayan an kammala taron.

Da duminsa: Buhari zai ziyarci kasar Chadi ranar Asabar

Da duminsa: Buhari zai ziyarci kasar Chadi ranar Asabar
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Khadimul islam: Ganduje ya rufe wani babban Otel a Kano, an kama masu karuwanci 19

Sanarwar ta cigaba da cewa za a karrama shugabanin kasashe da dakarun soji na kasashen Mali, Sudan, Somalia, Jamhuriyar Africa Ta Tsakiya da Tafkin Chadi.

Cikin wadanda za su yiwa shugaba Buhari rakiya akwai Gwamna Kashim Shettima na jihar Borno, Akinwunmi Ambode na jihar Legas da Adegboyega Oyetola na jihar Osun.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel