Bauchi: APC ta gabatar da rubutacciyar kara don kalubalantar nasarar Sanata Bala

Bauchi: APC ta gabatar da rubutacciyar kara don kalubalantar nasarar Sanata Bala

Jam’iyyar All Progressive Congress (APC) ta gabatar da rubutacciyar kara a kotun saurarron kararrakin zabe na jihar Bauchi, domin kalubalantar sakamakon zaben gwamna wanda Sanata Bala Abdulkadir Mohammed na jam’iyyar Peoples Democratic Party’s (PDP) ya lashe.

Jam’iyyar ta cike rubutacciyar karan ne a rana Juma’a, 12 ga watan Afrilu.

Da yake magana jim kadan bayan gabat da korafin, Shugaban APC na jihar Uba Ahmed Nana ya bayyana cewa sun gabatar da korafin ne don neman adalci.

Korafin da APC ta shigar shine na farko da ke kalubalantar zaben gwamna a jihar.

Bauchi: APC ta gabatar da rubutacciyar kara don kalubalantar nasarar Sanata Bala

Bauchi: APC ta gabatar da rubutacciyar kara don kalubalantar nasarar Sanata Bala
Source: UGC

Zuwa yanzu kotun sauraron kararrakin ta samu korafe-korafe 30 da ke kalubalantar sakamakon zabukan gwamna, na majalisar dattawa, na majalisar wakilai da kuma na majalisar dokokin jiha.

KU KARANTA KUMA: Ku tsayar da Alimikhena a matsayin mataimakin Shugaban majalisar dattawa – Aliu ga APC

A wani lamari makamancin haka, Legit.ng ta rahoto cewa kwana ashirin bayan bayyana Ganduje a matsayin wanda ya lashe zaben 23 ga watan Maris na gwamna a jihar Kano kamar yanda hukumar INEC ta sanar, jami’iyar PDP ta jihar ta shigar da kara tana mai nuna rashin amincewa da wannan nasara.

Karar kuwa da aka shigar na kalubalantar sakamakon zaben da aka sake yi ne inda take ikirarin cewa zabe na farko da akayi ranar 9 ga watan Maris Abba Yusuf shine yayi nasara don haka wannan sakamakon na baya sam bata aminta dashi ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel