Da duminsa: 'Yan bindiga sun kwace wa Gwamna Ajimobi Naira Miliyan 357

Da duminsa: 'Yan bindiga sun kwace wa Gwamna Ajimobi Naira Miliyan 357

An shiga rudani a jihar Oyo bayan wasu 'yan bindiga sun sace zunzurutun kudi Naira Miliyan 357 a yayin da ake kan hanyar tafiya da su wasu bankuna a garin Ibadan babban birnin jihar Oyo kamar yadda Sahara reporters ta ruwaito.

An fito da kudaden ne daga gidan Gwamna Abiola Ajimobi da ke unguwar Oluyole amma kudin bai isa inda za a kai ba yayin da 'yan bindigan suka tare motar da ke dauke da kudin suka kwace.

Majiyar Legit.ng ta fahimci cewa direban da ke tuka motar wani dattijo ne mai suna 'Baba Obe' wanda amintacce ne da ya dade yana yiwa iyalan Ajimobi hidima. A shekarun baya ma ya yi aiki a matsayin direban mahaifin Gwamna Ajimobi a lokacin da ya ke dan majalisar tsohuwar Majalisar Yammacin Najeriya.

Da duminsa: 'Yan bindiga sun kwace Gwamna Ajimobi N357m

Da duminsa: 'Yan bindiga sun kwace Gwamna Ajimobi N357m
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Zargin Madigo: Yadda Hadiza Gabon ta titsiye Amina Amal, ta rika zagba mata mari

Majiyar ta ce: "An fito da kudin ne cikin mota bus kirar Toyota Hiace kuma sun kan hanyarsu ne zuwa bankin Access da Heritage inda za su ajiye kudin amma sai wasu 'yan bindiga suka tare su a Ring Road kusa da hanyar Iyaganku zuwa Apata. Dukkan abin ya faru ne tsakanin 7.20 zuwa 7.35 na safiya."

Sahara Reporters ta ruwaito cewa 'yan bindigan sun yiwa mutumin da ke kula da kudaden mai suna Semiu rauni sakamakon dukarsa da su kayi da bindiga a kai.

Tuni dai an tsare Semiu saboda wasu daga cikin jiga-jigan gwamnatin jihar Oyo suna zargin akwai hannunsa cikin harin saboda babu wani na waje da ya san za a fita da kudaden zuwa banki.

Kakakin 'yan sandan jihar, Olugbenga Fadeyi ya ce bai da masaniya a kan afkuwar lamarin amma ya ce akwai yiwuwar harin ya faru sai dai ba a shigar da kara a ofishin 'yan sanda ba.

"Akwai yiwuwar an aikata fashi amma dai ba shigar da kara a ofishin 'yan sanda ba, idan ba a shigar da kara ba, babu yadda za mu san wani abu ya faru," inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel