Lawal, Ndume, Goje, duk sun cancanci jagorantar majalisar dattawa – Jigon APC

Lawal, Ndume, Goje, duk sun cancanci jagorantar majalisar dattawa – Jigon APC

- Jigon APC, Dr Umar Duhu ya bayyana cewa sanatoci uku da ke takarar shugabancin majalisar dattawa sun cancanta

- Duhu, mataimakin Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na farko a arewa maso gabas, ya nuna damuwa a gudanarwar shugabancin jam’iyyar

- Yace babu yadda za a yi jam’iyya ta tafiyar da ragamar mambobinta alhalin bata taka muhimmiyar rawar gani wajen tabbatar da zabarsu ba

Mataimakin Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na farko a arewa maso gabas, Dr. Umar Duhu, ya bayyana cewa dukkanin masu takaran kujerar Shugaban majalisar dattawa sun cancanci hawa matsayin.

Duhu wanda ya bayyana hakan a wata hira da jaridar Leadership, yace Sanata Ali Ndume da Sanata Ahmad Lawan sun fito daga kungiya daya na All Nigeria Peoples Party (ANPP), kuma dukkansu sun cancanci hawa kujeran.

Lawal, Ndume, Goje, duk sun cancanci jagorantar majalisar dattawa – Jigon APC

Lawal, Ndume, Goje, duk sun cancanci jagorantar majalisar dattawa – Jigon APC
Source: Facebook

Ya kuma bayyana cewa duk da cewar Sanata Danjuma Goje ya bito ne daga kungiya na daban, tsohon gwamnan na jihar Gombe ma ya cancanci zama Shugaban majalisar dattawa.

KU KARANTA KUMA: Shugabancin majalisa: Zamu yiwa masu butulci ritaya - APC

Ya kuma nuna tantama kan yadda shugabancin APC ke yi da wasu mambobinta, inda ya kara da cewa babu yadda za a yi jam’iyya ta tafiyar da ragamar mambobinta alhalin bata taka muhimmiyar rawar gani wajen tabbatar da zabarsu ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel