Buhari bai yi kokarin tsaida kashe-kashen da ake yi ba – Manyan Arewa

Buhari bai yi kokarin tsaida kashe-kashen da ake yi ba – Manyan Arewa

Manyan shugabanni da wasu masu fada-a-ji da ake da su yankin Arewacin Najeriya sun yi wani zama kwanan nan inda su ka tattauna a kan yawan kashe-kashen da ake gani a yankin a halin yanzu.

Kamar yadda Jaridar Vanguard ta dauko rahoto a yau 12 ga Watan Afrilu na 2019, wadannam manya sun fitar da matsaya na wannan zama da su kayi inda su kace lallai gwamnatin tarayyar Najeriya tayi kasa a gwiwa kan kare rayuka.

Dattawan na Yankin Arewa sun yi wannan zama ne a cikin Garin Zariya da ke jihar Kaduna inda a karshen wannan taro, babban jigo na kungiyar NEF ta Dattawan yankin watau Farfesa Abdullahi Ango ya fitar da wani rahoto.

Ango Abdullahi yake cewa akwai rashin ganin damar gwamnati na kawo karshen matsalar satar mutane da kuma ta’adin fashi da makami da rigimar makiyaya da manoma da ake ta fama da shi a yankin Arewacin Najeriya.

KU KARANTA: Farashin man fetur na iya kara tsada a Najeriya

Buhari bai yi kokarin tsaida kashe-kashen da ake yi ba – Manyan Arewa

Kungiyar NEF tayi zama a game da sha’anin tsaro a Arewa
Source: Depositphotos

Babban Farfesan yace bayan halin ko-oho na gwamnatin Najeriya, akwai kuma matsalar sace kudin tsaro, wanda duk ya taimaka wajen ganin har yau ba a iya shawo kan matsalolin da ake fama da su na kashe Bayin Allah ba.

Ango yake cewa bayan rikicin Boko Haram, ana fama da rikici tsakanin Makiyaya da Manoma, sannan kuma akwai matsalar garkuwa da mutane da fashi da kuma ta’adin da ake fuskanta daga wasu Miyagu masu kashe jama’a.

Farfesa Ango ya koka da yadda harkar noma ke fuskantar barazana a Arewacin kasar a halin yanzu, bayan nan kuma, rashin tsaron ya sa dole mutane sun koma gujewa tafiya a kan titunan yankin ana ji-ana gani saboda fashi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel