Ku tsayar da Alimikhena a matsayin mataimakin Shugaban majalisar dattawa – Aliu ga APC

Ku tsayar da Alimikhena a matsayin mataimakin Shugaban majalisar dattawa – Aliu ga APC

- Ga dukkan alamu Francis Alimikhena zai zamo mataimakin Shugaban majalisar dattawa na gaba

- Sanatan mai wakiltan yankin Edo ta arewa na ta samun tarin goyon baya daga mambobbin APC

- Wani jigon APC a babbar birin tarayya, ya shiga sahun masu kira ga tsayar da sanata Alimikhena

Mathias Aliu, zababben kansila na yankin Wuse, a babbar birnin tarayyar kasar, yace za a cuci yankin kudu idan har jam’iyyar All Progressives Congress (APC) bata tsayar da Sanata Francis Alimikhena a matsayin mataimakin Shugaban majalisar dattawa ba.

Alimikhena, wanda ya kasance jami’in soja mai ritaya kuma sanata a karo na biyu, na wakiltan yankin Edo ta arewa a majalisar dokokin kasar kuma shine mataimakin bulaliyar masu rinjaye a majalisar dattawa.

Ku tsayar da Alimikhena a matsayin mataimakin Shugaban majalisar dattawa – Aliu ga APC

Ku tsayar da Alimikhena a matsayin mataimakin Shugaban majalisar dattawa – Aliu ga APC
Source: Facebook

A wani jawabi da aka aikewa Legit.ng a ranar Juma’a, 12 ga watan Afrilu, Aliu yace sanatan na a matsayin da zai inganta ajandar jam’iyyar a kudancin kasar saboda kasancewarsa sanata mai kokari da fada aji.

KU KARANTA KUMA: Wata kungiya ta jinjina wa Buhari da hukumomin tsaro kan nasarar da aka samu a Zamfara da Yobe

Zababben kansilan ya bukaci zababbun sanatoci da su ajiye son zuciya sannan su duba cancanta da biyayya.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa mataimakin shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, yankin Arewa ta Tsakiya, Ahmed Wambai, ya bayyana cewa duk dan jam’iyyar ya yi adawa da hukuncin jam’iyyar dangane da zabin shugabancin majalisan dokokin kasar zai fuskanci hukunci akan rashin biyayya.

Mista Wambai, a wani hira da yayi da manema labarai a Lafia, ya bukaci mambobin jam’iyyar a majalisar dokoki da su yi biyayya ga hukuncin jam’iyyar a dukkan lokuta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel