Kotu ta tsare wani mutum aka zargin lalata da yar karamar yarinya

Kotu ta tsare wani mutum aka zargin lalata da yar karamar yarinya

Wata kotun majistare da ke Ebute-Meta, Lagas a ranar Juma’a, 12 ga watan Afrilu tayi umurnin tsare wani mutum mai suna Lukman Yekini kan zargin tarawa da karamar yarinya yar shekara 13.

Yekini, wanda aka ki amsa rokonsa, na fuskantar tuhume tuhume biyu na cin zarafi da kuma lalata.

Mai shari’a, Misis A.O. Salawu, ta tsare mai laifin a gidan kurkuku Ikoyi zuwa lokacin da sakamakon shawarar sashin hukunci na jiha zai fito.

Da farko, dan sanda mai kara, Sufeto Chinalu Uwadione, ya fada ma kotu cewa wanda ake karan ya aikata laifin ne a watan Fabrairu a Glover Estate da ke Ebute-Meta.

Kotu ta tsare wani mutum aka zargin lalata da yar karamar yarinya

Kotu ta tsare wani mutum aka zargin lalata da yar karamar yarinya
Source: Depositphotos

Uwadione yayi zargin cewa Yekini ya tara da yarinyar ta karfin tuwo.

KU KARANYTA KUMA: Ministar kudi ta amince da shawarar IMF kan cire tallafin mai

A cewarsa, laifin ya saba ma sashi na 137 da 411 na dokar laifi na jihar Lagas, 2015.

Mai shari’an ya dage sauraron karan zuwa ranar 8 ga watan Mayu.

A wani lamari makamancin haka mun ji cewa a irin kokarin da hukumar 'yan sandan Najeriya ta ke yi na kawo karshen mutane masu yiwa yara kanana fyade, hukumar ta kama wani mutum mai shakaru 65 ya yi wa wata yarinya 'yar shekaru 10 fyade da karfin tsiya.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, shi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a garin Abeokuta babban birnin jihar, ya ce sun kama wanda ake zargin ne, bayan mahaifin yarinyar Fahinhun Matthew ya kawo kara cewar wanda ake zargin makwabcinsa, ya aiki 'yar tashi, a lokacin da ta dawo sai ya tura ta cikin dakin shi ya yi mata fyade da karfin tsiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel