Kwamitiocin Majalisa ba su iya karasa aikin kasafin kudin 2019 ba

Kwamitiocin Majalisa ba su iya karasa aikin kasafin kudin 2019 ba

Mun samu labari cewa kwamitin da ke kula da harkar da ya shafi kasafin kudin Najeriya a majalisar dattawa sun gaza kammala aikin da aka daura a kan su a game da kasafin kudin wannan shekarar.

Kamar yadda labari ya zo mana a safiyar yau, Juma'a 12 ga Watan Afrilun 2019, wannan kwamiti bai kawo aikin da yayi gaban majalisa a zaman da aka yi a makon nan ba, kamar yadda Bukola Saraki ya bada umarni a baya.

Kwanakin baya, shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya nemi kwamitin kasafin da ya kammala duk aikin da ke gaban sa, sannan ya kawo rahoto a lokacin da za ayi zaman gama-gari a Majalisa a cikin farkon makon nan.

Sai dai a zaman da aka yi jiya, shugaban wannan kwamiti watau Mohammed Danjuma Goje bai iya mikawa majalisar wani rahoto ba. Alamu sun nuna cewa an samu bacin lokaci ne daga sauran kwamitocin majalisar.

KU KARANTA: Saraki ya fitar da bayanin kasafin kudin majalisa a bana

Kwamitiocin Majalisa ba su iya karasa aikin kasafin kudin 2019 ba

Sanata Goje bai kawo rahoton aikin kasafin kudi na bana ba
Source: Depositphotos

Rashin karasa aikin kasafin kudin a sauran kananan kwamitoci shi ya hana Sanata Danjuma Goje na APC mai wakiltar jihar Gombe ya iya mikawa majalisar dattawa babban rahoton da aka shirya karba a Ranar Talatar da ta wuce.

A Ranar Talatar ne dai ‘yan majalisar su ka amince da tsare-tsaren gwamnati na MTEF da FSP wandada za su taimaka wajen aiwatar da manufofin tattalin arzikin kasar. An kuma yi alwashin kammala aikin kasafin a makon gobe.

Har yanzu dai majalisar dattawan kasar tana kan bakatar ta ganin cewa an mikawa shugaban kasa Muhammadu Buhari kasafin kudin na 2019 ya sa hannu a kai a Ranar 16 ga Watan Afrilun nan.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel