Tsautsayi baya wuce ranarsa: Ruwa ya cinye wani karamin yaro a jahar Kano

Tsautsayi baya wuce ranarsa: Ruwa ya cinye wani karamin yaro a jahar Kano

Wani karamin yaro dan shekara 14, Huzaifah Abdulrashid ya gamu da ajalinsa a cikin wani korama mai suna ‘Promise’ dake titin Gwarzo na karamar hukumar Gwale ta jahar Kano, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta kaakakin hukumar kashe gobara ta jahar Kano, Saidu Mohammed ne ya bayyana haka a ranar Juma’a, 11 ga watan Afrilu, inda yace lamarin ya faru ne da safiyar Juma’a a lokacin da Huzaifah ya tafi wanka a tafkin.

KU KARANTA: Da dumi dumi: Kwankwaso zai tura yaran talakawa karatu zuwa kasashen waje

“Da misalin karfe 7:35 na safe muka samu labarin mutuwar Huzaifah daga bakin Malam Habibu Ibrahim, wanda ya bayyana mana cewa ya hangi gawar Huzaifah tana yawo a saman ruwa, ba tare da bata lokaci ba muka tura da jami’anmu zuwa bakin da misalin karfe 7:43.

“Koda jami’anmu suka isa sun tarar yaron ya rigamu gidan gaskiya, nan take suka afka cikin ruwan suka ciro gawarsa, inda suka mikata ga dakacin unguwar Dandago, Alhaji Abubakar Sani.” Inji shi.

Ana yawan samun jama’a da dama masu wanka a cikin tafkunan jahar Kano sakamakon halin matsanancin zafin yanayi da ake ciki a Kano, wanda hakan ke yin sanadin mutuwar wasu daga cikinsu idan lamarin yazo da tsautsayi.

A wani labarin kuma, ajali ya kira wani matashi mai suna Musa dan shekara 22 daya mutu a wani tafki dake cikin unguwar Farawa Ramin Fara, a karamar hukumar Tarauni na jahar Kano, kamar yadda kaakakin hukumar kwana kwana, Saidu Mohammed ya bayyana haka a ranar Laraba, 10 ga watan Afrilu.

Malam Saidu ya bayyana cewa wannan lamari mai ban ta’ajibi ya faru ne da tsakar ranar Laraba yayin da matashin ya shiga cikin tafkin don yin wanka sakamakon tsananin zafin yanayi da ake fama dashi a Kano.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel