Shekaru 5 da sace yan matan Chibok: Muhimman batutuwa 10 game da harin Chibok

Shekaru 5 da sace yan matan Chibok: Muhimman batutuwa 10 game da harin Chibok

Kimanin shekaru biyar kenan tun bayan harin da mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram suka kai makarantar sakandarin ta kwana na yan Mata dake karamar hukumar Chibok ta jahar Borno, inda suka yi awon gaba da dalibai mata dari biyu da saba’in da shida.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wasu daga cikin yan matan guda sittin sun tsere daga hannun mayakan na Boko Haram a lokacin da suke kan hanyar tafiya dasu, yayin da kungiyar ta sako wasu yan mata 100 daga cikinsu.

KU KARANTA: Da dumi dumi: Kwankwaso zai tura yaran talakawa karatu zuwa kasashen waje

Shekaru 5 da sace yan matan Chibok: Muhimman batutuwa 10 game da harin Chibok

Yan matan Chibok
Source: Twitter

Ga dai wasu daga cikin muhimman bayanai game da satar nay an matan Chibok kamar haka;

- A ranar 14 ga watan Afrilu na shekarar 2014 ne yan Boko Haram suka sace yan makatan Chibok su 276

- Boko Haram ta kashe sama da mutane 20,000 tun shekarar 2009 da suka fara kokarin kafa daular Musulunci

- Boko Haram sun sace sama da mata da kananan yara 4000 tun daga shekarar 2009, da suke amfani dasu a matsayin bayi, sadaka da harin kunar bakin wake

- An kaddamar da gwagwarmayar sako yan matan na #BringBakcOurGirls a shekarar 2014

- A watan Mayu na shekarar 2016 aka fara ceto guda daga cikin yan matan, Amina Ali da danta

- A watan Oktoban 2016 kungiyar ta sako yan mata 21 bayan Malam Zannah Mustapha ya tattauna da kungiyar

- A watan Mayun 2017 kungiyar ta sako wasu yan mata 82 bayan an sako musu manyan kwamandojinsu

- A watan Janairun 2018 Boko Haram ta fitar da bidiyon wasu yan Mata 5 da yayansu da sukace ba zasu koma ga iyayensu ba

- Boko Haram sun sako wata Mata mai suna Jumai mai shekaru 35 data bayyana cewa ta ga yan matan Chibok a watan Oktoban 2018

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel