Sojoji sun kashe yan bindiga guda 23, sun ceto mutum 40 a jihar Zamfara

Sojoji sun kashe yan bindiga guda 23, sun ceto mutum 40 a jihar Zamfara

Sojojin da suke gudanar da atisaye 'Sharan Daji' da ke jihar Zamfara sun kashe yan bindiga guda 23 sannan kuma sun kama mutane 18 da ake zargin suna da hannu wurin taimakawa yan bindigan, makiyaya, masu garkuwa da mutane da kuma yan ta’adda a jihar.

Kakakin sojan Sharan Daji, Clement Abiade, a wani jawabi yake cewa sojojin sama sun kai hari a dazukan Kagara, Gando, Fankama, Fete da Dumburum.

Har ila yau, Muhammed Isa, yana daya daga cikin masu garkuwa da mutanen da aka kama a kasar Niger tare da hadin gwiwar jami’an tsaro na kasar.

Dan bindigan dan asalin garin Naagwalam ne dake jihar Katsina kuma ya tona kanshi cewar yana daya daga cikin masu garkuwa da mutane da kuma yan fashi a mahadar Batsari da Jibiya.

An mikashi ga jami’an tsaro dan tsatsauran bincike.

Abiade yace: “Atisayen da aka kai cikin dajin ya kai ga an ceto rayukan mutane 40 wadanda suka hada da magidanta, mata da kananan yara daga cikin kauyuka dake jihar Zamfara".

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel