Yanzu-yanzu: Saraki ya fitar da bayanin kasafin kudin majalisa na 2018

Yanzu-yanzu: Saraki ya fitar da bayanin kasafin kudin majalisa na 2018

Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya fitar da bayanan kasafin kudin majalisa na shekarar 2018 ga al'ummar kasa.

Shugaban majalisar ya bayar da umurnin a fitar da bayanan kasafin kudin ne bayan matsin lamba da cibiyar sa ido na BudgIT da dade tana masa.

Saraki ya yi amfani da shafinsa na sada zumunta na Twitter @SPNigeria a ranar Juma'a ya fadawa BudgIT cewar ga bayanin kasafin kudin.

Dala-dala: Saraki ya fitar da bayanin kasafin kudin majalisa na 2018

Dala-dala: Saraki ya fitar da bayanin kasafin kudin majalisa na 2018
Source: UGC

Duba bayanin dala-dala kamar yadda majalisar ta fitar.

DUBA WANNAN: Khadimul islam: Ganduje ya rufe wani babban Otel a Kano, an kama masu karuwanci 19

A wata labarin, Legit.ng ta kawo muku cewa wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta dakatar da yanke hukunci a kan karar da wata kungiya, 'Legal Defence and Assistance Project (LEDAP)', ta shigar a kan neman a kori shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, da wasu sanatoci 55.

LEDAP ta shigar da karar Saraki da ragowar sanatoci 55 bisa hujjar cewar su ba mambobin majalisar dattijai ba ne saboda sun canja sheka zuwa wasu jam'iyyu kafin karewar wa'adinsu. Kungiyar, a takardar karar da suka shigar, sun nemi kotu ta fassara sashen 68(1)(g) na kundin tsarin mulki na shekarar 1999.

Sashen na da alaka da batun matsayin mamba a majalisar tarayya bayan ya fita daga cikin jam'iyyar da ya ci zabe kafin karewar zangonsa. Kungiyar na neman kotun ta bayyana mambobin a matsayin haramtattu, sannan su mayar wa da gwamnatin tarayya dukkan alabashi da alawus-alawus da suka karba bayan sun canja sheka.

A cikin takardar karar, LEDAP ta nemi kotu ta tilasta shugabannin majalisa su bayyana duk wanin mamba da ya canja sheka a matsayin haramtacce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel