Dole a cigaba da tuhumar Onnoghen duk da ya yi murabus - BMO

Dole a cigaba da tuhumar Onnoghen duk da ya yi murabus - BMO

- Wata kungiyar magoya bayan Buhari, BMO ta bukaci a cigaba da shari'ar tsohon Alkalin alkalai Walter Onnoghen

- A cikin sanarwar da ta fitar, BMO ta ce cigaba da shari'ar Onnoghen ne zai zama hujja bisa dakatar da shi da shugaba Muhammadu Buhari ya yi a baya

- Kungiyar ta ce murabus din ta tsohon Alkalin alkalai Onnoghen ya yi nasara ce ga yaki da cin hanci da rashawa

Kungiyar magiya bayan Buhari, 'Buhari Media Organisation' (BMO) ta bukaci a cigaba da shari'ar tsohon Alkalin Alkalai na kasa, Justice Walter Samuel Onnoghen.

Sanarwar da kungiyar ta fitar a ranar Alhamis 9 ga watan Afrilu ta hannun jagoran kungiyar, Niyi Akinsiju da sakataren kungiyar, Cassidy Madueke ta ce murabus din Onnoghen ba zai zama dalili na dakatar da shari'ar ba.

Dole a cigaba da tuhumar Onnoghen duk da ya yi murabus - BMO

Dole a cigaba da tuhumar Onnoghen duk da ya yi murabus - BMO
Source: UGC

DUBA WANNAN: Zargin Madigo: Yadda Hadiza Gabon ta titsiye Amina Amal, ta rika zagba mata mari

A yayin da kungiyar ta jinjinawa hukumar yaki da rashawa, EFCC da kotun da'ar ma'aikata, CBB bisa kokarin da su kayi na bibiyar shari'ar, kungiyar ta bukaci a cigaba shari'ar tsohon Alkalin.

A cewar BMO, cigaba da shari'ar za ta zama hujja bisa dakatar da shi da shugaba Muhammadu Buhari ya yi a baya.

Sanarwar ta ce: "Wannan za ta bawa dakataccen tsohon Alkalin alkalan damar kare kansa a kotu kana ta bawa shugaba Muhammadu Buhari cikaken hujjar da zai kafa na dakatar da Onnoghen idan an same shi da laifi a maimakon a bari 'yan adawa su rika amfani da damar suna cewa an tilastawa Onnoghen ficewa daga ofis ne.

"Hakan kuma za ta zama darasi ga wasu bara gulbin da ke bangaren shari'a bisa himmar gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari na yaki da rashawa."

Bayan cacakan wasu kafafen watsa labarai da ke sukar shari'ar ta Onnoghen, kungiyar da ce murabus din da tsohon Alkalin Alkalan ya yi nasara ce ga yaki da rashawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel