Ministar kudi ta amince da shawarar IMF kan cire tallafin mai

Ministar kudi ta amince da shawarar IMF kan cire tallafin mai

Ministar kudi, Misis Zainab Ahmed, a ranar Alhamis, 11 ga watan Afrilu ta bayyana shawarar da kungiyar IMF ta ba Gwamnatin Tarayya akan bukatar janye tallafin mai a matsayin abu mai kyau.

Yayinda take magana a taron IMF da bankin duniya a Washington D.C, ta ce: shawarar da ya fito daga IMF akan batun janye tallafin mai abune mai kyau amman kuma ya kamata a aiwatar da shi ta yanda za a cimma nasara da dorewa.

“Bama a cikin yanayin da za mu wayi gari wata rana sannan kawai a janye tallafin mai. Dole mu ilimantar da mutane, dole mu nuna ma yan Najeriya ayyukun da zasu maye gurbin tallafin mai. Muna da ayyuka da dama da zamu gudanar. Akwai kuma bukatar fahimtar cewa ba a cire makuden kudade na tallafin mai a lokaci guda, dole ya kasance a hankali sannan dole al’umma ta kasance sane da ayyukan da za a gudanar”.

Ministar kudi ta amince da shawarar IMF kan cire tallafin mai

Ministar kudi ta amince da shawarar IMF kan cire tallafin mai
Source: Depositphotos

Bayanai daga ofishin kula da basussuka ya nuna cewa jimmilar bashin Najeriya ya tashi zuwa naira tiriliyan 24.39 ko dala biliyan 79.44 a ranar 31 ga watan Disamba 2018, sannan sun nuna tashi na shekara da shekara da kashi 12.25. Bashin 2018 ya fi na shekara 2017 da naira biliyan 2.662.

Misis Ahmed tace shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umurci minister da ta bincika duk fannin dake bukatar gyare gyare.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Sokoto mai zuwa na bukatar addu’a – Inji hadimin Tambuwal

Ministar tace Gwamnatin Tarayya ta bukaci Bankin Duniya da ta sake duba wasu shirye shiryen da ta tanadar, har da wadanda ya shafe su, ganin tsarin aiwatarwa a fannonin da suke samar da kudi don aiwatar da ayyuka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel