Shehu Sani ya bayyana dalilin da zai sa yayi nasara a kotun zabe

Shehu Sani ya bayyana dalilin da zai sa yayi nasara a kotun zabe

- Wani mamba a majalisar dattawa, Shehu Sani, ya kaddamar da cewar zai samu adalci a kotun sauraron kararrakin zabe

- Sani ya tunkari kotun zabe domin kalubalantar faduwarsa a zaben da ya gabata

- Dan majalisan yace zai gabatar da hujja a inda bukatar hakan ta taso don tabbatar da lamarin

Sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya a majalisar dokokin kasar, Shehu Sani, ya nuna tabbacin samun nasara a kararsa da ke kalubalantar sakamakon zaben majalisar dokoki a jihar.

Jaridar Guardian ta ruwaito cewa dan majalisan yace daga cikin dalilan shigar da karan shine don neman adalci da kuma gabatar da hujja a inda ya kamata domin tabbatar da shari’an.

Shehu Sani ya bayyana dalilin da zai sa yayi nasara a kotun zabe

Shehu Sani ya bayyana dalilin da zai sa yayi nasara a kotun zabe
Source: Depositphotos

Legit.ng ta rahoto cewa Sani ta hannun lauyansa, Kafas Kure, yace yana sauraron samun adalci a karshen shari’an.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Sokoto mai zuwa na bukatar addu’a – Inji hadimin Tambuwal

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa Kotun da aka kafa domin sauraron korafe korafen zaben gwamnan jihar Sokoto ta amince da wata bukata ta jam'iyyar APC, ta hannun lauyanta, Dr. Alex Iziyon SAN, na barin jam'iyyar duba kayayyakin da aka yi amfani da su a zabukan jihar na ranar 9 da 23 ga watan Maris.

Jam'iyyar APC da dan takararta, Alhaji Ahmed Aliyu Sokoto, sun shigar da kara gaban kotun inda suke kalubalantar nasarar da gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jam'iyyar PDP ya samu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel