Shugabancin majalisa: APC ta yiwa Ndume nasiha kan muhimmancin biyaya

Shugabancin majalisa: APC ta yiwa Ndume nasiha kan muhimmancin biyaya

Jam'iyyar All Progressives Congress (APC), reshen jihar Yobe ta shawarci Sanata Ali Ndume ya mutunta zabin jam'iyya a kan ra'ayin kansa domin samun maslaha a jam'iyyar da majalisar baki daya.

Sakataren watsa labarai na jam'iyyar reshen jihar Yobe, Alhaji Abubakar Bakabe ne ya yi wannan kirar yayin zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na kasa, NAN a ranar Juma'a a garin Damaturu.

"Jam'iyya tana gaba da kowa," inji Alhaji Bakabe.

Ya gargadi Ndume a kan hada kai da jam'iyyar adawa domin yiwa jam'iyyar APC zagon kasa.

DUBA WANNAN: Zargin Madigo: Yadda Hadiza Gabon ta titsiye Amina Amal, ta rika zagba mata mari

Shugabancin majalisa: APC ta yiwa Ndume nasiha kan muhimmancin biyaya

Shugabancin majalisa: APC ta yiwa Ndume nasiha kan muhimmancin biyaya
Source: Depositphotos

"Ya kamata Ndume ya yi takatsantsan da irin tarkon da majalisa za ta iya kafa masa, bai dace mu bari abinda ya faru a lokacin shugabancin Saraki ya sake faruwa ba saboda cigaban jam'iyya, Najeriya da demokradiyya," inji shi.

Ya yabawa sabbin zababun 'yan majalisan da suka bayar da goyon bayan game da zabin jam'iyyar da fadar shugaban kasa a kan batun shugabancin majalisar.

"Jam'iyyar APC reshen jihar Yobe tana fatan sanata Ndume zai cigaba da yiwa jam'iyya da fadar shugaban kasa Muhamadu Buhari biyaya.

"A matsayin mu na jam'iyya, ba za mu amince wata matsala da raba kawunnan mu ba bayan wahalhalun da muka sha a shekaru hudu da suka gabata.

"Zabin Sanata Lawan Ahmed domin shugabancin majalisa zai samar da ingantaccen shugabanci da APC ke bukata domin aiwatar da shirye-shiryen da za su amfani al'ummar Najeriya.

"Lawan zai yi aiki tare da kowa ba tare da nuna banbanci ba. Yana da kwarewa da gogewa a fannin tafiyar da mulki da ake bukata a majalisa," inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel