An kama wani tsoho ya yiwa 'yar shekara 10 fyade

An kama wani tsoho ya yiwa 'yar shekara 10 fyade

A irin kokarin da hukumar 'yan sandan Najeriya ta ke yi na kawo karshen mutane masu yiwa yara kanana fyade, hukumar ta kama wani mutum mai shakaru 65 ya yi wa wata yarinya 'yar shekaru 10 fyade da karfin tsiya

Hukumar 'yan sandan jihar Ogun ta kama wani mutumi mai suna Sulaiman Rauf dan shekara 65, da laifin yi wa yarinya 'yar shekara 10 fyade.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, shi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a garin Abeokuta babban birnin jihar, ya ce sun kama wanda ake zargin ne, bayan mahaifin yarinyar Fahinhun Matthew ya kawo kara cewar wanda ake zargin makwabcinsa, ya aiki 'yar tashi, a lokacin da ta dawo sai ya tura ta cikin dakin shi ya yi mata fyade da karfin tsiya.

An kama wani tsoho ya yiwa 'yar shekara 10 fyade

An kama wani tsoho ya yiwa 'yar shekara 10 fyade
Source: UGC

Ya ce: "Lokacin da yarinyar ta fito daga dakin wanda ake zargin, sai ta sanar da mahaifinta abinda mutumin ya yi mata.

Bayan mutumin ya kai rahoton, sai DPO ofishin 'yan sandan CSP Aloko Amodu, ya umarci jami'an 'yan sanda su je su kamo wanda ake zargin.

KU KARANTA: Atiku na cikin tsaka mai wuya

A lokacin da ake tuhumar wanda ake zargin, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce sharrin shaidan ne ya ja shi aikata wannan mummunan aiki.

A yanzu haka dai an kai yarinyar asibitin domin tabbatar da lafiyar ta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel