An ba wa Buhari wata daya ya sanya hannu akan dokar karin albashi

An ba wa Buhari wata daya ya sanya hannu akan dokar karin albashi

- Kungiyar kwadago ta kasa ta bawa shugaban kasa Muhammadu Buhari wata daya ya sanya hannu akan dokar karin albashi

- Kungiyar ta ce ta na so shugaban kasar ya shigar da dokar kafin ranar bikin murnar ma'aikata ta duniya ta zagayo

Kungiyar kwadago ta kasa ta nuna damuwarta akan jinkirin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ke yi wurin saka hannu a dokar karin albashi ga ma'aikata.

Dokar wacce za ta bai wa ma'aikatan Najeriya damar samun karin albashi, inda za a dinga biyan mafi kankanta akan naira 30,000, dokar da majalisar tarayya ta riga ta mika ta zuwa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, yanzu shi ake jira kawai ya sanya hannu. A wata hira da aka yi da Sakatare Janar na kungiyar Peter Ozo-Eson, ya bayyana cewa jinkirin da shugaban kasar ya ke yi yayi yawa.

An ba wa Buhari wata daya ya sanya hannu akan dokar karin albashi

An ba wa Buhari wata daya ya sanya hannu akan dokar karin albashi
Source: Depositphotos

Ya ce 'yan Najeriya sun kosa suga shugaban kasar ya tabbatar da dokar, wacce za ta kawo cigaba ga rayuwan al'ummar kasar nan.

Ozo-Eson, ya bukaci shugaban kasar ya sanya hannu akan dokar, kafin ranar ma'aikata ta duniya ta zagayo, wacce za ayi a cikin watan Mayu.

KU KARANTA: Atiku na cikin tsaka mai wuya

Ya ce: "Munyi tunanin abu ne wanda shugaban kasa zai yi murna da shi kuma, ya shigar da shi dokar kasa cikin gaggawa, saboda kamar yadda muka bayyana muna so wannan dokar ta fara aiki kafin watan Mayun da zamu shiga.

Saboda haka muna kira ga mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya sanya hannu akan dokar cikin gaggawa, ko da ma'aikata za su fara amfana da karin da aka yi musu kafin ranar bikin murnar ma'aikata ta duniya."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel