Gwamnatin Sokoto mai zuwa na bukatar addu’a – Inji hadimin Tambuwal

Gwamnatin Sokoto mai zuwa na bukatar addu’a – Inji hadimin Tambuwal

- Yusuf Dingyadi na son mutanen Sokoto su yiwa gwamnatin jihar mai zuwa addu’a

- Dingyadi yayi alkawarin cewa gwamnatin Gwamna Tamuwal na biyu zai fi na farko inganci

- Hadimin gwamnan yayi godiya da shugabanin addini da sarakuna akan goyon bayansu ga ci gaban jihar

Mista Yusuf Dingyadi, babban mataimakin Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, akan ayyuka na musamma, ya bukaci mutanen jihar da su gudanar da addu’an nasara ga gwamnati mai zuwa.

A wani jawabin da Dingyadi ya gabatar a Sokoto a ranar Alhamis, 11 ga watan Afrilu yayi kira ga zaman lafiya, tarayya, biyayya ga juna da yarda da juna akan ra’ayoyin siyasa.

Ya bada tabbacin cewa mulkin Tambuwal na biyu zai fi na farko inganci da tarin ci gaba.

Gwamnatin Sokoto mai zuwa na bukatar addu’a – Inji hadimin Tambuwal

Gwamnatin Sokoto mai zuwa na bukatar addu’a – Inji hadimin Tambuwal
Source: Twitter

Har ila yau, Dingyadi, ya gargadi mambobin adawa da su guji yin fada da gwamna da mambobin jam’iyya mai mulki.

KU KARANTA KUMA: Shugabancin majalisa: Zababbun sanatocin PDP na shirin billowa APC ta bayan gida

Ya yaba ma shuwagabannin addini da na kauyuka akan goyon baya da addu’o’i don nasarar gwamnatin Tambuwal, ya kuma bukace su da kada suyi wargi.

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Sarkin Kano Muhammad Sanusi II, ya bayyana cewa sun gama shirye-shirye tsaf na gabatar da dokar tsarin tazarar haihuwa ga gwamna Abdullahi Umar Ganduje, domin mai da tsarin doka a jihar Kano.

Sarkin ya bayyana hakan a wurin wani taron tattaunawa da suka gabatar a Kano, ya ce za a gabatar da tsarin ne don magance kalubalen da ake fama dashi a kasar Hausa na tsarin iyali, da kumaa matsalar tsaron da ake fama da ita a yankuna da dama na kasar nan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel