Shugabancin majalisa: Zababbun sanatocin PDP na shirin billowa APC ta bayan gida

Shugabancin majalisa: Zababbun sanatocin PDP na shirin billowa APC ta bayan gida

Rikici mai karfi na ci gaba da billowa a sansanonin zababbun sanatoci da ke fafutukar neman shugabancin majalisar dattawa, a majalisar dokokin kasar na tara wanda za a rantsar a watan Yuni.

A yanzu haka, wasu mambobin majalisar adawa ta PDP, wadanda suka kasance zababbun sanatoci ke shawartan takwarorinsu da su jure duk wani fitina na neman kujerar mataimakin Shugaban majalisar dattawa.

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa wasu sansani a PDP sun yanke shawarar cewa a mataki da sanatocin APC uku suka nace kan neman kujerar Shugaban majalisar dattawa, jam’iyyar adawar za ta taru sannan ta gabatar da dan takara daya da zai samu kuri’un PDP.

Rikici yayinda sanatoci APC ke faftukar neman shugabancin majalisar dokokin kasar

Rikici yayinda sanatoci APC ke faftukar neman shugabancin majalisar dokokin kasar
Source: Depositphotos

Kasancewar ta kwace wasu jihohi daga hannun jam’iyyar APC mai mulki a zaben kwanan nan da aka kammala, an tattaro cewa PDP na ganin za ta iya kokari ba tare da ta samu kujerar mataimakin Shugaban majalisar dattawa ba a majalisa ta tara, wanda wasu ke ganin zai taimaka masu wajen samun cikakken adawa ga jam’iyyar APC mai mulki, idan har kokarinsu na kwace zaben Shugaban kasa bai zo da nasara ba a kotu.

An tattaro cewa wasu zababbun sanatocin PDP, na neman wani mafita cewa idan APC ta gaza daidaita gidanta, inda Sanata Danjuma Goje, Ahmed Lawan da Ali Ndume suka raba mafi akasarin kuri’un APC, za su tsayar da dan takara a majalisar sannan su bashi kuri’unsu domin ya zama Shugaban majalisar dattawa.

KU KARANTA KUMA: Buratai ya jinjina wa dakarun soji bayan sun fatattaki yan ta’addan Boko Haram a Damaturu

Wani dan majalisa, wanda ya caccaki takwarorinsa na PDP da ke hararar kujerar mataimakin Shugaban kasa, yace jam’iyyar APC ce za ta yanke hukunci kan wanda zai riki mukamin Shugaban marasa rinjaye a majalisar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel