Babban magana: An cafke 'Farfesa' a dakin rubuta jarabawar JAMB

Babban magana: An cafke 'Farfesa' a dakin rubuta jarabawar JAMB

Jami'an Hukumar Tsaro ta NSCDC sun cafke wani mutum da ya yi ikirarin cewa shi Farfesa ne mai suna Jide a ranar Alhamis 11 ga watan Afrilu a unguwar Jabi da ke babban birnin tarayya Abuja.

An kama shi ne bayan ya yi nasarar yin kutse cikin dakin rubuta jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire, JAMB domin ya taimakawa diyarsa rubuta jarabawar.

Mai magana da yawun hukumar JAMB, Dr Fabian Benjamin ya ce hukumar NSCDC za ta gurfanar da Jide a gaban kuliya domin ya fuskanci hukunci kan laifin da ya aikata.

DUBA WANNAN: Zargin Madigo: Yadda Hadiza Gabon ta titsiye Amina Amal, ta rika zagba mata mari

Cakwakiya: An cafke 'Farfesa' yana rubuta jarabawar JAMB

Cakwakiya: An cafke 'Farfesa' yana rubuta jarabawar JAMB
Source: Depositphotos

Ya ce: "Wani mutum ya yi kutse ya shiga dakin rubuta jarabawar JAMB a Brix Academy da ke Jabi domin ya taimaki diyarsa. A lokacin da aka kama shi, ya yi ikirarin cewa shi Farfesa ne kuma yana da wata gidauniya na tallafawa al'umma.

"Jami'an tsaro sun kama shi kuma yana tare da su. Muna kyautata zaton za a gurfanar da shi a kotu cikin kankanin lokaci.

"An kama shi kafin ya samu damar aikata mummunan abinda ya yi niyyar yi. Ya yi ikirarin cewa shi farfesa ne a wata jami'a da ke kasar waje."

Benjamin ya kuma ce an samu nasara wurin rubuta jarabawar ta JAMB a ranar Alhamis duk da cewa an samu wasu kallubalai a wasu wurare inda ya ce yana fatan abubuwa za su inganta.

Dalibai 1,855,643 za su rubuta jarabawar ta JAMB a bana daga ranar Alhamis zuwa ranar Litinin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel