Faduwa zabe ba kanka aka fara ba, Gwamnatin tarayya ta fadawa Atiku

Faduwa zabe ba kanka aka fara ba, Gwamnatin tarayya ta fadawa Atiku

-Atiku yayi hayar wasu yan Amurka domin su taimak masa wajen nuna rashin amincewa da zaben 2019 da akayi.

-Haryanzu Atiku yaki rungumar faduwa zaben da yayi a matsayin kaddara, a nashi ganin shine ya lashe zabe ba Buhari ba.

Gwamnatin tarayya tace dan takarar PDP, Atiku Abubakar yana da damar da zai kalubalanci nasarar Shugaba Muhammadu Buhari akan zaben 2019 a kotu. Kari akan hakan tayi kira ga tsohon mataimakin shugaban kasan da ya bari kotun ta yi abinda ya dace bisa ga baiwa wanda ya dace nasara ko kuma karar tasa ta gaza yin wani tasiri.

Tace Atiku yayi kuskuren ganin cewa baya bukatar taimakon kowa yana tunanin cewa shi zai iya baiwa kansa nasarar da yake neman a zaben. Gwamnatin ta kara da cewa yakamata Atiku ya san cewa faduwa zabe ba fa tashin duniya bane.

Buhari da Atiku

Buhari da Atiku
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Shugabancin majalisa: Zababbun sanatocin PDP na shirin billowa APC ta bayan gida

Ministan yada labarai, Alhaji Lai Mohammed da yake tsokaci ga manema labarai akan matsayar gwamnati kan lamarin a Abuja ranar Alhamis yayi suka ga hotunan Atiku da aka sanya a wasu wurare a birnin Abuja dauke da rubutun 'NA GASKEN, MAI GIRMA ATIKU ABUBAKAR, KAINE DAI NA GASKEN GASKE' wanda ya karade wasu titunan birnin Abuja.

Yace “Tabbas, Atiku ya fadi zabe. Sai dai ba zai taba zama farau ko karau ba akan wannan lamari don haka yakamata ya gane faduwa zabe ba wai tashin duniya bane. Ya kalubalanci sakamakon zaben a kotu. Wannan abu ne da yake dai dai. Kada ya kasance ya karaya bisa karar da ya shigar ta hanyar debe tsanmanin samun nasara daga wurin kotun, wanda har yasa yake nema yayi mai gaban kansa.

“Ya dace ya natsu ya kuma daina daukan abin da zafi kwarai domin kada hakan ya haifar da barkewar rikicin siyasa a Najeriya. Babu wani dan kasa da yafi karfin doka koda kuwa wane matsayi gareshi. Abin ya isa haka.”

Mohammed wanda yake tare da babban mai taimkawa shugaban kasa akan harkokin labarai, Mallam Garba Shehu, yace hotunan da aka sanya da kuma zargin cewa anyi hayar yan kasar Amurka abin zargine akan abinda Atiku ke niyyar yi.

Yace, “Shin ko yana sake sabon kamfe ne bayan an kammala zabe an samu wanda yayi nasara da kuma wanda ya fadi? Ya janye kudurinsa na shigar da kara gaban kotu, bayan ya tabbatar cewa sakamakon da yake tinkaho dashi na shafin INEC a yanar gizo ba sahihi bane? Shin yanzu zai nemi taimaikon kansa ne ta wata hanyar? Ko kuma me Atiku ke shirin yi ne?

“Muna sane da cewa dan takarar shugaban kasar ya nisanta kan shi daga hotunan dake yawo a birnin Abuja ranar Laraba. Haka kuma ya karyata zarginsa da ake na cewa ya dauko hayar yan Amurka yace wannan maganar shaci fadi ce da fito daga bakin APC.

“Idan abinda ake fadi a kafofin sadarwa ya kasance gaskiyane to lallai tsohon mataimakin shugaban kasan ya fahimci kuskuren dake cikin abinda yake da niyyar aikatawa domin hakan ne ma yaja baya kafin lokaci ya kure masa.

“A matsayinshi na gogaggen dan siyasa yakamata ya san cewa hanyar kawai da zai iya bi don nuna rashin amincewarsa da wannan zabe itace kawai ta shigar da kara kotu. Dukufa akan wata hanyar da ba wannan ba bata ma kai lokacine kawai da kuma nuna wutar ciki kan wannan lamari.

“Alhaji Atiku Abubakar yanada damar yabi duk hanyoyin da basu sabawa shari’a ba domin ya kalubalantar wannan zabe. Amma ba zai iya biyowa ta bayan fage ba kuma ya samu abinda yake bukata. Wannan shi ake kira karancin tunani.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel