Buratai ya jinjina wa dakarun soji bayan sun fatattaki yan ta’addan Boko Haram a Damaturu

Buratai ya jinjina wa dakarun soji bayan sun fatattaki yan ta’addan Boko Haram a Damaturu

- Laftanal-Janar Tukur Buratai, Shugaban hafsan soji, ya aika sakon jinjina ga dakarun sojojin da suka yi kasa-kasa da yan ta’addan Boko Haram a Damaturu, jihar Yobe

- Shugaban sojin Najeriyan ya bukaci dakarun sojin da su ci gaba da kasancewa kwararru sannan su lallasa yan ta’addan

- A ranar Talata, 9 ga watan Afrilu, dakarun sojin sun dakile wani hari da yan ta’addan suka yi yunkurin kaiwa garin Maisandari da ke jihar ta Yobe

Shugaban rundunar sojin Najeriya, Laftanal-Janar Tukur Buratai, a ranar Alhamis, 11 ga watan Afrilu ya yabi jajajircewar rundunar bisa nasarar da suka yi akan yan kungiyan Boko Harama kauyen Maisadari da ke wajen birnin Damaturu, Yobe.

A wani jawabinsa daga mataimakin Datektan sadarwa na rundunar Sector 2 Operation Lafiya Dole, Lt. Njoka Irabor, ya bayyana cewa yabon ya zo ne ta hannun kwamandan tiyata na rundunan, Manjo Janar Benson Akinroluyo, a ranar Alhamis a Damaturu.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ta rahoto cewa a ranar Talata rundunar tayi nasarar dakile harin da yan ta’addan suka yi yunkurin kai wa kauyen Maisandari, inda rundunar ta kashe yawancinsu tare da tarwatsa kayan aikinsu.

Akinroluyo, wanda yayi jawabi ga rundunar a hedikwatan 233 Battalion, duk da haka ya yabi rundunar sojin sama da sauran hukumomin tsaro, har da al’umma masu biyayya ga doka akan goyon baya da hadin kai wanda ya jagorancin ba yan ta’addan kashi.

Buratai ya jinjina wa dakarun soji bayan sun fatattaki yan ta’addan Boko Haram a Damaturu

Buratai ya jinjina wa dakarun soji bayan sun fatattaki yan ta’addan Boko Haram a Damaturu
Source: Depositphotos

Ya bukaci rundunar da su kara kaimi don tabbatar da yin nasara wajen yaki da ta’addanci.

KU KARANTA KUMA: Isra’ila ta mayar da masallaci mai cike da tarihi zuwa mashaya da wajen taro

Shugaban rundunar ya karfafa bukatar hada hannu da hadin kai a kokari tsakanin runduna da sauran hukumomin tsaro don hana yan ta’addan yancin gudanar da ayyukansu.

Akinroluyo ya samu jawabai daga hannun kwamandan 233 Battalion, Laftanal Kanal Ibrahim Mohammed.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel