Rundunar sojin sama ta bukaci wanda suka yada rahoton ta kashe mutanen gari su gabatar da shaida

Rundunar sojin sama ta bukaci wanda suka yada rahoton ta kashe mutanen gari su gabatar da shaida

- Bayan zargin da sarakunan gargajiya suka yi akan rundunar sojin saman Najeriya, na cewa sun kashe mutanen da ba su da laifi

- Rundunar sojin saman ta nunabacin ranta akan sarakunan gargajiyan, inda ta bukaci su gabatar da shaidu akan zargin da suke

Rundunar sojin saman Najeriya (NAF) ta yi kira ga duk wani wanda yake da shaida da ke nuna cewa sun kashe mutanen da ba 'yan ta'adda ba a jihar Zamfara da ya fito ya bayyana shaidar shi.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar sojin saman Air Commodore Ibikunle Daramola, shine ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja a yau juma'ar nan. Ya bukaci duk wani wanda ya ke da shaida da ya fito ya gabatar da ita.

Daramola ya ce rundunar sojan saman ba ta ji dadin irin wannan zargin da ake yi mata ba, kuma bata yi tunanin wani zai je ya dinga yada irin wannan labarin kanzon kuregen ba, ganin yadda rundunar ta ke aiki kai da kafa wurin ganin ta kawo karshen matsalar tsaro a jihar Zamfara dama kasa baki daya.

Rundunar sojin sama ta bukaci wanda suka yada rahoton ta kashe mutanen gari su gabatar da shaida

Rundunar sojin sama ta bukaci wanda suka yada rahoton ta kashe mutanen gari su gabatar da shaida
Source: Facebook

Rundunar sojin saman ta na magana ne akan wani rahoto da aka fitar da ya ke nuni da cewa wani hari da rundunar ta kai karkashin rundunar soja mai taken 'Operation Diran Mikiya' harin na su ya kashe mutanen gari ne, wadanda ba 'yan ta'adda ba.

Rundunar sojin ta bayyana cewa bata ji dadin wannan rahoto ba, saboda yawancin inda ta kaiwa hari na kusa da yankin dajin Rugu, Sububu, da kuma dajin Kagara, wanda kowa ya san wannan wuri ne da 'yan ta'addar suke buya a ciki, kuma an sha kai musu hari wurin, ba tare da wata matsala ba.

KU KARANTA: Buratai ya yi karin haske akan kashe-kashen jihar Zamfara

A cewar jami'in rundunar sojin, wuraren da suka kaiwa harin a ranar 8 da ranar 11 ga watan Afrilun nan, sai da hukumar ta gama tantance wurin tsaf ta hanyar yin amfani da na'ura mai kwakwalwa, da kuma amfani da bayanan da mutane suke bawa rundunar kafin rundunar ta kaiwa wurin hari.

A cewarshi, rundunar sojin sama ba ta kaiwa wuri hari mutukar tana da bayanin cewa wurin akwai mata ko yara wadanda basu da laifin komai, wanda hakan doka ce ga duk wani jami'in rundunar.

Daramola ya ce rundunar sojin saman ba ta son ta samu wata matsala da kowanne mutum, musamman ma sarakunan gargajiya, saboda haka ta na bukatar duk masu yada irin wannan jita-jita da su kyale rundunar ta yi aikinta yadda ya kamata, domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a cikin al'ummar Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel