Majalisa ta gayyaci shugaban kasa ya gurfana gabanta akan kashe kashen Zamfara

Majalisa ta gayyaci shugaban kasa ya gurfana gabanta akan kashe kashen Zamfara

Majalisar wakilan Najeriya ta umarci shugaban kasa Muhammadu Buhari daya gurfana a gabanta domin ya bayyana ma yan Najeriya dalilin kashe kashen dake aukuwa a fadin Najeriya, tare da bayyana mata hanyoyin da yake bi don shawo kan matsalar.

Majalisar ta bayyana haka ne a zamanta na ranar Alhamis, inda tace idan kuwa har Buhari yaki gurfana a gabanta, hakan zai tabbatar da ra’ayin yan Najeriya dake ganin gwamnatin Najeriya ta gaza wajen karesu da dukiyoyinsu.

KU KARANTA: Kabiru Marafa ya yi ma Saraki tayin kyakkyawar budurwa sakamakon tallafa ma Zamfara

Majalisa ta gayyaci shugaban kasa ya gurfana gabanta akan kashe kashen Zamfara

Majalisa ta gayyaci shugaban kasa ya gurfana gabanta akan kashe kashen Zamfara
Source: UGC

Majiyar Legit.ng ta ruwaito dan majalisa mai wakiltar mazabar Gwer ta gabas da Gwer ta yamma na jahar Benuwe, Mark Gbillah ne ya gabatar da wannan kuduri ga majalisar, kuma ya samu goyon bayan akasarin yan majalisar.

Kudurin mai taken ‘farfadowar kashe kashen Najeriya babu kakkautawa a Najeriya’ ya tabo yadda yan bindiga da makiyaya ke samun gindin zama a Najeriya suna kashe jama’a babu ji babu gani, tare da jefa wasu cikin mawuyacin halin gudun hijira.

Da wannan ne majalisar ta baiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari wa’adin kwanaki biyu ya gurfana a gabanta don ya tsatstsage mata bayanin duk abinda ya sani game da matsalar tsaron da Najerya ke fuskanta a yanzu.

“Ya kamata Buhari ya bayyana dalilin da yasa bai bayyana makiyaya dake kai hare hare a matsayin yan ta’adda ba, ta yadda Sojoji zasu daman daukan matakin daya dace akansu. Dalilin da yasa Sojoji suka gaza magance asarar rayukan yan Najeriya a hannun yan bindiga.

“Dalilin da yasa yake nuna halin ko kula tare da nuna son kai a duk lokacin da yan bindiga suka kai hari a wasu wurare, musamman a wasu bangaren Najeriya, musamman jahar Benuwe, da kuma matakan da yake daukan don magance matsalar.” Inji shi.

Daga karshe majalisar ta yanke shawarar kafa kwamiti na musamman da zata goga gemu da gemu da fadar shugaban kasa, sa’annan zata gana da ministan tsaro, Mansur Dan Ali, manyan hafsoshin tsaro, gwamnatocin jahohi da sauran masu ruwa da tsaki.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel