An kashe mutane 10 a jihar Binuwai

An kashe mutane 10 a jihar Binuwai

- Rikicin kabilar Tiv da Jukum dai ya ki ci ya ki cinyewa a jihar Binuwai

- A jiya ne makiyaya da suka hada kai da kabilar Jukum su ka kai wa wani kauye hari, inda suka kone gidaje masu yawan gaske sannan suka kashe mutane 10

A kalla mutane 10 ne aka kashe a wani hari da aka kai kauyen Vaase a karamar hukumar Ukum da ke cikin jihar Binuwai.

Majiyarmu LEGIT.NG ta samu rahoton cewa an kaiwa mutanen da suke zaune akan iyakar jihar Binuwai da jihar Taraba hari a safiyar jiya.

Mai bai wa gwamnan jihar Binuwai shawara a fannin tsaro, Col. Paul Hemba, ya tabbatar da cewar ya samu rahoton cewa an kashe mutane tsakanin 8 zuwa 10, a harin da aka kai kauyen.

Hemba ya ce a rahoton da ya samu, an bayyana mishi cewar wadanda suka kai harin sun hada da 'yan kabilar Jukun da kuma makiyaya.

An kashe mutane 10 a jihar Binuwai

An kashe mutane 10 a jihar Binuwai
Source: Facebook

Ya bayyana cewa ya tuna lokacin da ya kaiwa hukumar 'yan sanda rahoton cewa ya samu labarin makiyaya suna shirin kaiwa kauyen Vaasee hari, satin da ya gabata.

Ya ce a lokacin jami'an 'yan sandan sunje sunyi bincike a yankin ranar Laraba, inda suka bayyana cewa zasu aika da jami'an 'yan sanda su lura da wurin ranar Alhamis, sai dai kuma an kai harin ne kafin jami'an 'yan sandan suje wurin.

KU KARANTA: Buratai ya yi karin haske akan kashe-kashen jihar Zamfara

Hemba ya ce lamarin ya faru duk da irin kokarin da gwamnatin jihar ta ke yi na kawo karshen rikicin a fadin jihar.

Ya roki mutanen kauyen su kwantar da hankulansu, inda ya bayyana musu cewa hukuma ta dauki mataki akan lamarin, ya bayyana cewa akwai gidaje akalla guda 100 da aka kone, sannan sama da mutane 3,000 'yan kabilar Tiv da ke jihar Taraba sun kauracewa gidajen su, sun gudu jihar Binuwai da garuruwa da ke makwabtaka da jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel