Bai dace ba ga kowane asibiti su ki karbar wanda suka samu hadari, inji hukumar kiyaye hadurra ta FRSC

Bai dace ba ga kowane asibiti su ki karbar wanda suka samu hadari, inji hukumar kiyaye hadurra ta FRSC

-Rashin karabar wanda hatsari ya rutsa da su da asibitoci keyi sam bai kamata ba

-Ceto rayukan wadanda suka jikkata da samun rauni shine abinda yakamata ya zamo kan gaba kafin duk wani bayani ya biyo yayin da hatsari ya auku

Hukumar kiyaye hadurra ta kasa FRSC, ta bakin jagoran sashen yankunan jihohin Sokoto, Kebbi da Zamfara, Dr Kayode Olagunju ya gargadi asibitoci da su guji rashin karbar wadanda hatsari ya shafa.

“Ya sabawa doka a wurin ko wace asibiti ta aikata hakan”, a cewarsa.

Da yake ganawa da gangamin masu tattara bayanan da suka shafi al’amuran da suka shafi hadurra akan titunan yankin wato ‘Road Traffic Crashes,RTC’ , ya ce za’a cisu tarar naira dubu hamsin da kuma daurin wata shida a gidan yari ga masu aikita wannan danyen aiki.

FRSC akan aiki

FRSC akan aiki
Source: Depositphotos

KU KARANTA:Majalisa ta gayyaci shugaban kasa ya gurfana gabanta akan kashe kashen Zamfara

Olagunju ya bayyana muhimmancin ceto rayuwar wanda suka jikkata, ganin cewa hakan shine abu da yafi dacewa ayi domin tabbatar da cewa ba’a rasa rayukan jama’ar da abin ya shafa ba cikin awa daya da aukuwar hatsarin.

Ya sake fadin cewa: “Dole ne a kasnace an dukufa cikin shiri domin ganin cewa an ceto rayukan wadanda suka jikkata musamman cikin wannan awa dayan mai matukar amfani.

“Bisa ga tsarin kulawa da ake amfani dashi a duniya yanzu, kamata yayi ace RTC na aiki na tsawon kwana talatin a wata domin gudanar da aikin ceto rayuka wadanda suka samu hatsari kana kuma wadanda suka rasa rayukansu ya zamana cewa RTC na sane da mutuwarsu bal ma sun rasu ne karkashin kulawar tasu.

Ya sake neman dukkanin kungiyoyin da abin ya shafa da su hada kai wajen gudanar aikinsu da ya shafi rage aukuwar hadurra akan tituna. Ya sake kuma neman hukomin da ke da alaka da RTC kamarsu, FRSC,Yan sanda, asibitoci, hukumar binciken ababen hawa, hukumar kididdiga da hasashe ta kasa da su kasance a kan aiki ko wane lokaci domin daukar duk wani abu da ka iya faruwa a rubuce.

Olagunju ya shawarcesu da suyi aiki tukuru domin samarwa RTC ingantaccen bayani wanda zasu adana a cikin inda suke aje harkokin da suka shafi aikinsu.

A karshe kuma ya janyo hakalin ‘National Road Traffic Crash Management System, NRTCMS’ da suke tara bayanai dake aukuwa da suka shafi hadurra na kasa da ya zama daya dana RTC ba tare da sun bambamta ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel