Artabun Sojoji da Boko Haram: Buratai ya jinjina ma dakarun Sojin Najeriya

Artabun Sojoji da Boko Haram: Buratai ya jinjina ma dakarun Sojin Najeriya

Babban hafsan Sojan kasa, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai ya bayyana godiyarsa, tare da jinjina ma dakarun rundunar mayakan Sojan kasa bisa jarumtar da suka nuna a Damaturu, babban birnin jahar Yobe a lokacin da mayakan Boko Haram suka yi kokarin kutsawa garin.

Mataimakin kaakakin rundunar Sojan kasa na Operation Lafiya Dole, Laftanar Njoka Irabor ne ya sanar da haka a ranar Alhamis, 11 ga watan Afrilu, inda yace kwamandan Operation Lafiya Dole, Manjo janar Benson Akinroluyo ne ya mika wannan sako a madadin Buratai.

KU KARANTA: Kabiru Marafa ya yi ma Saraki tayin kyakkyawar budurwa sakamakon tallafa ma Zamfara

Legit.ng ta ruwaito a ranar Talatar data gabata ne mayakan rundunar Sojan kasa suka samu galaba akan mayakan Boko Haram a wata arangama da suka yi a kauyen Maisandari lokacin da suka yi kokarin kutsawa cikin garin Damaturu.

A yayin wannan karanbatta dai Sojoji sun karkashe yan Boko Haram da dama, tare da lalata motocin yakinsu, yayin da sauran suka tsere da kafafuwansu dauke da rauni daban daban, tare da jefar da makamansu.

Manjo Janar Benson ya mika wannan jinjina a madadin Buratai ne yayin da yake ganawa da dakarun Soji a shelkwatar bataliya ta 233, inda ya bayyana jin dadin babban hafsan sojan kasan da wannan nasara, tare da mika gadiyarsa ga Sojojin sama, jama’an gari da sauran hukumomin tsaro da suka bada gudunmuwar karya yan ta’addan.

Hala zalika Janar Benson ya nemi Sojojin dasu cigaba da jajircewa don ganin sun kawar da yan Boko Haram gaba daya a jahar Yobe, dama yankin Arewa maso gabas gaba daya, don haka yace akwai bukatar hadin gwiwa tsakanin rundunar da sauran hukumomin tsaro don hana Boko Haram sakat.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel