A karshe, gwamna Wike ya roki Amaechi da APC a jihar Ribas

A karshe, gwamna Wike ya roki Amaechi da APC a jihar Ribas

- Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya roki tsohon jihar, Rotimi Amaechi, da su hada hannu wajen ciyar da jihar Ribas gaba

- Kazalika, gwamnan ya roki jam'iyyar APC a kan su hada kai domin yin aiki tare domin kishin jihar Ribas

- Gwamna Wike ya yi alkawarin jagorantar gwamnati da za tayi tafiya da kowa domin cigaban jihar Ribas ba tare da la'akari da jam'iyya, kabila ko addini ba

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya roki ministan harkokin sufuri, Rotimi Amaechi, da jam'iyyar APC, da su bashi hadin kai domin ciyar da jihar Ribas gaba.

Gwamnan ya yi wannan roko ne yayin jawabi da ya gabatar a ranar Alhamis, 11 ga watan Afrilu, bayan kotun koli ta yi watsi da karar da APC a jihar Ribas ta shigar, kamar yadda jaridar Vanguard ta rawaito.

Wike ya yi alkawarin jagorantar gwamnati da za tayi tafiya da kowa, ya ce ribar ta jihar Ribas ce idan duk shugabanni da jagororin jam'iyyu da jama za su hada kai.

A karshe, gwamna Wike ya roki Amaechi da APC a jihar Ribas

Wike da Amaechi
Source: UGC

Ya ce: "na san cewar irin wannan siyasar ta gaba da kiyayya ta samo asali ne daga wasu abubuwa da suka faru a baya, na yi amanna cewar za mu iya inganta rayuwar jama'ar mu tare da kawo cigaba ga jihar mu idan muka hada kai

DUBA WANNAN: Son kai kawai aka nuna a zaben gwamnan Kano - Abba Gida-Gida

"A saboda haka, ina kira ga jam'iyyar APC da jagoranta a jihar Ribas, Ministan harkokin sufuri, Rotimi Amaechi, da su zo mu hada hannu wuri guda domin cigaban jihar mu. Ba zai yiwu a matsayin mu na shugabanni mu kawo wa jihar mu cigaba ba idan babu hadin kai.

"Ni a nawa bangaren, na yi alkawarin hada kai da duk wasu shugabanni da jagororin siyasa da jama'a a jihar Ribas domin cigaban jiha da jama'a, zan yi hakan ba tare da la'akari da banbancin jam'iyya, kabila ko addini ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel