Sojoji sun mayar da mutane fiye 4,000 gidajensu a Jakana

Sojoji sun mayar da mutane fiye 4,000 gidajensu a Jakana

Kimanin mutum 4, 927 da ke zaune a garin Jakana, jihar Borno, rundunar soji ta mayar gidajensu a jiya bayan da farko sun kwashe su zuwa Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

A ranakun Talata da Laraba ne rundunar soji tare da ragowar jami'an tsaro suka kwashe kafatanin mazauna garin Jakana a karamar hukumar Konduga domin samun damar fatattakar 'yan ta'adda da ke yankin.

Mayakan Boko Haram na amfani da garin Jakana mai nisan kilomita 48 daga Maiduguri domin shiga babban birnin na jihar Borno. Garin ya na kan hanya Maiduguri zuwa Damaturu.

Sojoji sun mayar da mutane fiye 4,000 gidajensu a Jakana

Sojoji
Source: Twitter

Kungiyoyin bayar da agajin gaggawa na kasa da jihar Borno da ragowar kungiyoyin aikin jin kai sun bi sahun jami'an soji wajen nuna murnar mayar da mutanen garin Jakana gidajensu a jiya.

DUBA WANNAN: Dole ka yi magana a kan matsalar Zamfara, mun ba ka sa'a 48 - 'Yan majalisa ga Buhari

"NEMA ta tattara kayan abinci da sauran kayan amfani domin raba wa ga jama'ar Jakana da aka dawo da su," kamar yadda kakakin NEMA a Maiduguri, Abdulkadir Ibrahim, ya sanar jim kadan bayan dawo da mutanen gidajensu.

Ibrahim ya ce NEMA ta yi hakan ne domin tallafa wa mutanen bayan samu katsewar harkokin kasuwanci sakamakon hijirar da suka yi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel