Son kai kawai aka nuna a zaben gwamnan Kano - Abba Gida-Gida

Son kai kawai aka nuna a zaben gwamnan Kano - Abba Gida-Gida

Abba Gida-Gida, dan takarar gwamnan jihar Kano karkashin inuwar jam'iyyar PDP, yayin wata hira da sashen Hausa na gidan radiyon BBC ya ce ba zabe aka yi zagaye na biyu na kammala zaben kujerar gwamna a jihar Kano.

Da ya ke magana a yammacin ranar Alhamis bayan shigar da korafinsa a gaban kotun sauraron karar zabe da ke zaman ta a kan titin Miller na unguwar Bompai a cikin birnin Kano, Abba ya ce an hada baki da jami'an tsaro da na hukumar zabe wajen cin amanar dimokradiyya da mutanen jihar Kano.

Abba ya kara da cewa sam ba zasu amince da sakamakon zaben ba, saboda duniya ma ta san ba zabe aka yi a jihar Kano ba.

"An kori wakilan jam'iyyar mu daga rumfunan zabe, an ci zarafin jama'a, da suka hada da 'yan jrida. Kuma duk an yi haka ne da hadin bakin jami'an tsaro da ma su kan su jami'an hukumar INEC," a cewar Abba.

Son kai kawai aka nuna a zaben gwamnan Kano - Abba Gida-Gida

Abba Gida-Gida
Source: UGC

Sannan ya kara da cewa, a zaben farko na ranar 9 ga watan Maris da INEC ta gudanar, jam'iyyar PDP ce a gaba, amma sai aka ce zaben bai kammalu ba don kawai a samu damar murde nasarar da PDP ta samu.

DUBA WANNAN: Wasu kungiyoyi 4 sun bukaci EFCC ta kwace wani jirgin sama mallakar tsohon ministan PDP

Ya ce hakan ne yasa da aka zo zagaye na biyu, suka zabi su nuna son-kai tunda sun san in dai zabe za a yi ba zasu samu nasara ba.

Kazalika ya bayyana cewar sun zo kotun sauraron korafin zabe ne domin gabatar da hujjojin da lauyoyinsu suka kammala tattara wa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel