Wasu kungiyoyi 4 sun bukaci EFCC ta kwace wani jirgin sama mallakar tsohon ministan PDP

Wasu kungiyoyi 4 sun bukaci EFCC ta kwace wani jirgin sama mallakar tsohon ministan PDP

Wasu kungiyoyi hudu da ke rajin kare hakkin bil adama sun rubuta takardar neman hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC) da ta kwace wani jirgin sama mallakar tsohon ministar man fetur a lokacin mulkin Obasanjo, Cif Dan Etete.

Kungiyoyin sun ce jirgin, wanda aka yi kiyasin cewar ya kai dalar Amurka $56m, an saye shi ne da kudin badakalar sayar da rijiyar man fetur mai lamba OPL 245.

Sun bayyana cewar jirgin tsohon ministan na da lamabar mallaka kamar haka; M-MYNA.

Takardar neman kwace jirgin, da kungiyoyin suka aiko wa shugaban hukumar EFCC daga kasar Italy, na dauke da sa hannun Olarenwaju Suraju; shugaban wata kungiya mai suna 'Human Resources Development Centre (HEDA)', Nick Hildyard; darektan wata kungiya mai suna 'Corner House, Antonio Tricarico da Simon Taylor na kungiyar 'Global Witness'.

Wasu kungiyoyi 4 sun bukaci EFCC ta kwace wani jirgin sama mallakar tsohon ministan PDP

Shugaban hukumar EFCC; Ibrahim Magu
Source: Depositphotos

Kungiyoyin hudu, a cikin wani jawabi da suka fitar ranar Alhamis a birnin Milan na kasar Italy, sun bayyana cewar sun samu hujjojinsu ne daga tuhumar badakalar sayar da rijiyar man fetur da ake yi a kotun kasa da kasa da ke Milan, Italy.

Binciken badakalar sayar da rijiyar man fetur mai lamba OPL 245 ga kamfanin 'Eni and Shell' ya shafi tsofin shugabanni, 'yan siyasa da manajojin kamfanoni a Najeriya da wasu kasashen ketare.

DUBA WANNAN: Dole ka yi magana a kan matsalar Zamfara, mun ba ka sa'a 48 - 'Yan majalisa ga Buhari

A cikin takardar da suka aika wa EFCC, shugabannin kungioyin hudu, sun bayyana cewar jirgin tsohon ministan ya na kasar Dubai, sannan sun bukaci gwamnatin Najeriya ta gudanar da bincike domin tabbatar da hakan.

Kazalika, sun bukaci gwamnatin Najeriya ta hada kai da mahukunta a ksar Dubai domin samun damar karbo jirgin, wanda suka ce da dukiyar Najeriya tsohon ministan ya saye shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel