An damke yan Najeriya 33 a kasar Kenya

An damke yan Najeriya 33 a kasar Kenya

- Kuma dai! Wasu yan Najeriya sun sake abin kunya a kasae ketare

- Wannan karon a wata kasar Afrika na bata kai Najeriya daraja ba suka kunyata kasar

- An gurfanar da su a kotu

Hukumar yan sandan jihar Kenya ta damke wasu matasa yan Najeriya guda 33 da aka kama suna zaune a kasar ba bisa doka ba.

An damke wadannan matasa ne ranar Alhamis, a garin Kasarani dake Nairobi, babbar birnin kasar Kenya, inda aka ruwaito cewa sun shiga kasar a kwanaki daban-daban.

KU KARANTA: Harin rundunar sojin sama alummar gari kawai ta kashe ba yan bindiga ba

Kwamandan hukumar yan sandan yankin Kasaran, Peter Kamani, ya bayyanawa manema labarai cewa jami'an yaki da muggan kwayoyi da suka kama wadannan matasa yayinda suka fita sintirin masu safarar muggan kwayoyi.

Peter Kimani ya ce matasan sun kasance suna amfani da takardan shaidar bogi na makarantun International University-Africa (USIU) da jami'ar Kenyatta, alhalin suna niyyar sayar da kwayoyi ne.

Yace: "Yayinda suka shigo, sun bayyana cewa su dalibai ne a jami'a amma bincikenmu ya nuna cewa sun shigo ne domin haramtattun kasuwanci."

An gurfanar da su gaban kotun Kiambu, yayinda ake shirin mayar dasu Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel