Harin rundunar sojin sama alummar gari kawai ta kashe ba yan bindiga ba

Harin rundunar sojin sama alummar gari kawai ta kashe ba yan bindiga ba

Rundunar sojin sama ta kashe alumman gari ne kawai ba yan bindiga ba a kananan hukumomi da kauyuka biyar, cewar majalissar sarakunan gargajiya ta jihar Zamfara.

Shugaban majalisar sarakunan gargajiyar, sarkin Bungudu, Alhaji Hassan Attahiru, wanda yayi magana da yawun sarakunan ya fadawa manema labarai cewa sojin saman basu taba samun galaba ba akan yan bindiga ba.

Rahoto daga hudu daga cikin kananan hukumomin Zurmi, Tsafe, Gusau da Anka sun nuna cewa biyar daga cikin kauyukan da sojin saman suka kai hari bai kashe yan bindiga ba cewar shugabannin gargajiyan kawai,alummar gari harin ya afkawa.

KU KARANTA: Garkuwa da mutane: Hanyar Kaduna zuwa Abuja ta gyaru yanzu - IG Adamu ga matafiya

Kana sarakunan sun yi Allah wadai da maganan da ministan tsaro, Masur Janar, yayi na cewa wasu sarakunan gargajiya ke goyon bayan barandanci.

Majalisar sarakunan jihar Zamfara sun karyata zargin da ministan tsaro, Mansur Dan Ali yayi a kansu; cewa wasu sarakuna a jihar na da hannu a ayyukan yan bindiga a jihar.

Mai kawo wa Legit.ng rahoto a Zamfara, Lawal Tsalha, ya rahoto cewa an bayyana hakan en a ranar Alhamis, 11 ga watan Afrilu, biyo bayan wani taron gaggawa da majalisar sarakunan jihar ta gabatar a ma’aikata kananan hukuma da lamuran sarauta.

Kakakin majalisar, Sarkin Bungudu, Alhaji Muhammad Attahiru, yayi kira ga ministan tsaron da ya kira sunan sarakunan da ke da hannu a fashin kamar yadda yake a zarginsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Online view pixel