Abba ya shigar da Ganduje kara kotu bisa nasarar da ya samu

Abba ya shigar da Ganduje kara kotu bisa nasarar da ya samu

-Abba ya maka Ganduje kara a kotun sauraren korafin zabe, jam'iyar PDP a jihar Kano tace zaben ranar 9 ga watan Maris kawai ta sani.

-PDP a jihar kano na kalubalantar nasarar Abdullahi Umar Ganduje

Kwana ashirin bayan bayyana Ganduje a matsayin wanda ya lashe zaben 23 ga watan Maris na gwamna a jihar Kano kamar yanda hukumar INEC ta sanar, jami’iyar PDP ta jihar ta shigar da kara tana mai nuna rashin amincewa da wannan nasara.

Karar kuwa da aka shigar na kalubalantar sakamakon zaben da aka sake yi ne inda take ikirarin cewa zabe na farko da akayi ranar 9 ga watan Maris Abba Yusuf shine yayi nasara don haka wannan sakamakon na baya sam bata aminta dashi ba.

Ganduje da Abba

Ganduje da Abba
Source: UGC

KARANTA WANNAN:An samu rahoton barkewar cutar sankarau har guda 4 a Bauchi

Jam’iyar tana ganin sake zaben da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa tayi a matsayin wani al’amari wanda ya sabawa dokar kasa da kuma kundin tsarin mulki.

Da yake Magana da yan jarida jim kadan bayan shigar da karar a kotun dake sauraren korefe-korefen zabe, Yusuf yace yayin da aka gudanar da zabe a ranar 9 ga watan Maris jam’iyar PDP ita ce kan gaba a ilahirin kananan hukumomi 44 da ke fadin jihar.

“Fatanmu a nan shine kotu ta fadi hakikanin wanda yayi nasara a zaben ranar 9 ga watan Maris. Ni dai a matsayina na dan takarar jam’iyar PDP zabe daya na sani wanda akayi ranar 9 ga watan Maris kawai.”

Ya sake cewa batun sake gudanar da wani zabe na daban abu ne wanda ya sabawa shari’a a ganin jam’iyarsu ta PDP ‘wanda kuma sam basu aminta dashi ba.

Lauyan da ya jagoranci karar tasu, mai suna Maliki Kuliya-Umar, yace sanarwar cewa zaben 9 ga watan Maris bai kamala ba dama ce kawai aka baiwa APC domin ta murde zaben ta kuma sake daura dan takararta bisa kan mulki.

“Muna kyautata zaton cewa kotun za tayi adalci domin ta tabbatar da hakikanin wanda ya lashe wannan zaben ranar 9 ga watan Maris saboda shi kadai ne sahihin zabe wanda shari’a da kuma doka ta aminta dashi.”

Umar yace duk wani dalili da ya sanya hukumar zabe fadin cewa sakamakon zaben 9 ga wata bai kammala ba daliline wanda ya sabawa doka bisa ga la’akari da kundin tsarin dokokin zabe.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel