Tsohon kakakin kungiyar Boko Haram ya shigar da karar shugaban DSS da AGF

Tsohon kakakin kungiyar Boko Haram ya shigar da karar shugaban DSS da AGF

Wata babbar kotun gwamnatin tarayya da ke zamanta a unguwar Maitama, Abuja, ta tsayar da ranar 23 ga watan Mayu domin fara sauraron karar neman kudin fansar wahalar wa, N500,000, da tsohon kakakin kungiyar Boko Haram, Ali Sanda konduga, ya shigar.

Kwanduga ya shigar da karar babban darektan hukumar tsaro ta farin kaya da ministan shari'a na kasa, bisa zarginsu da take masa hakkinsa na dan bil adam.

Konduga, ta hannun lauyansa, Mista Mohammed Tola, sun shigar da kara a gaban Jstis Samira Bture bisa zargin cewar an kara tsare shi na tsawon wasu shekaru bayan ya kammala zaman gidan yari na wasu shekaru ukun kafin a sake shi a 2016

Wata kotun majisatare ce ta yanke wa Konduga hukuncin daurin shekara uku bayan samunsa da laifin yin barazanar ta'addanci a sheakarar 2011.

Tsohon kakakin kungiyar Boko Haram ya shigar da karar shugaban DSS da AGF

Konduga
Source: Twitter

A cikin takardar karar, Konduga ya yi ikirarin cewar an ajiye shi a ofishin DSS sabanin gidan yari da kotu ta yanke hukuncin a tura shi, saboda gwamnati na son yin amfani da shi a matsayin shaida a tuhumar aikata ta'addanci da take yiwa Sanata Ali Ndume a wata babbar kotun Abuja.

DUBA WANNAN: Dole ka yi magana a kan matsalar Zamfara, mun ba ka sa'a 48 - 'Yan majalisa ga Buhari

Ya kara da cewa har ya zuwa lokacin da aka sake shi, ba a taba kiransa domin bayar da shaida a kan shari'ar ba.

Konduga ya ce hukumar DSS ta bawa iyalinsa N700,00 domin a kula da lafiyar sa bayan an sake shi.

Kyautar kudin, a cewar Konduga ta nuna karara cewar hukumar DSS ta san cewa ya kamata a biya shi diyyar kudin tsare shi da aka yi, ya kara da cewa hukumar ta DSS ta ki bashi wata diyya bayan N700,000

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel