Zaben gwamnan Rivers: Kotun koli ta yi watsi da bukatar APC na kan sanya 'yan takara

Zaben gwamnan Rivers: Kotun koli ta yi watsi da bukatar APC na kan sanya 'yan takara

- A karo na biyu, kotun koli ta yi watsi da bukatar PC na amincewa da 'yan takararta cikin jerin 'yan takarar da suka yi zabe a jihar Rivers

- Kotun ta bayyana cewa daukaka karar da APC ta yi bai cancanta ba, babu hujjojin dogaro akai, don haka kotun ta yi watsi da karar

- Rahotanni sun bayyana cewa jam'iyyar APC ba ta gudanar da zaben fitar da gwani na jihar Rivers akan lokaci ba

A karo na biyu, kotun koli ta yi watsi da bukatar da jam'iyyar APC ta gabatar mata na amincewa da 'yan takararta shiga cikin jerin 'yan takarar da suka yi zabe a jihar Rivers.

Kotun ta yi watsi da daukaka karar da jam'iyyar APC ta yi na rokon kotun da ta jingine hukuncin da ta fara yi wanda ya yi watsi da hukuncin da karamar kotun ta yi na haramtawa APC gabatar da 'yan takara a zaben 2019 saboda rashin cancanta.

Wani kwamiti mai mambobi 7 daga masu shari'a a kotun kolin bisa jagorancin mukaddashin alkalin alkalai na kasa Mai shari'a Tanko Muhammad, a hukuncin da suka yanke, sun bayyana cewa daukaka karar da APC ta yi bai cancanta ba, babu hujjojin dogaro akai, don haka kotun ta yi watsi da karar.

KARANTA WANNAN: Buhari ya gaggauta kubutar da Leah Sharibu daga hannun BH - Majalisar dattijai

Zaben gwamnan Rivers: Kotun koli ta yi watsi da bukatar APC na kan sanya 'yan takara

Zaben gwamnan Rivers: Kotun koli ta yi watsi da bukatar APC na kan sanya 'yan takara
Source: Twitter

Jam'iyyar APC a cikin wata takardar daukaka kara, ta hannun lauyanta, Justin Okutepa SAN, ta bukaci kotun kolin da ta warware hukuncin da ta yanke a baya na cewar APC ba za ta iya gabatar da 'yan takara ba saboda ta karya dokar kotun daukaka kara da ke Fatakwal, saboda ta shigar da karar a kurarren lokacin da ya wuce ka'ida.

Ya kuma bukaci kotun kolin da ta soke sashe na 22 da ta yi hukunci akansa tare jinginar da hukuncin da babbar kotun jihar Rivers ta yi wanda ya haramtawa APC shiga cikin babban zaben kasar akan cewar ba ta gudanar da sahihin zaben fitar da gwani ba.

Sai dai, lauyan jam'iyyar PDP, Emmanuel Ukalla SAN, a cikin wata sanarwa ta kin amincewa da bukatar dayan bangaren, ya bukaci kotun kolin da ta kori wannan kara da APC ta daukaka akan rashin kwararan hujjoji da kotun za ta dogara da su.

Da suke yanke hukunci akan shari'ar, kwamitin alkalan bakwai sun amincewa da hujjojin da lauyan PDP ya gabatar tare da watsi da daukaka karar jam'iyyar APC saboda rashin madogara.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel